1 Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga wani tauraron da ya faɗa a kan duniya daga sama, aka ba shi mabuɗin ramin mahallaka.
2 Ya kuwa buɗe ramin mahallakar, sai wani hayaƙi kamar na babbar matoya ya taso, har hayaƙin ramin nan ya duhunta rana da sararin sama.
3 Fāri suka fito zuwa cikin duniya daga cikin hayaƙin nan, aka ba su ikon harbi, irin na kunamin duniya.
4 Aka kuwa hana su cutar ciyayin duniya, ko tsiro, ko kowane itace, sai dai mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu.
5 Aka kuwa yardar musu su yi musu azaba har wata biyar, amma kada su kashe su, azabarsu kuwa, kamar ta kunama take, in ta harbi mutum.
6 A waɗannan kwanaki kuwa mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su same ta ba, za su ƙagauta su mutu, mutuwa kuwa sai ta guje musu.
7 Kamannin fārin nan kuwa kamar dawakai ne da suka ja dāgar yaƙi, a kansu kuma da wani abu kamar kambin zinariya, fuskarsu kuwa kamar ta mutum,
8 gashinsu kamar na mace, haƙorinsu kuma kamar na zaki.
9 Suna saye da sulkuna kamar na ƙarfe, dirin fikafikansu kuwa kamar dirin kekunan doki masu yawa ne suna rugawa fagyan yaƙi,
10 wutsiyarsu kamar ta kunama, ga kuma ƙari, ikonsu yana ji wa mutane ciwo har wata biyar kuwa a wutsiyarsu yake.
11 Sarkinsu kuwa da yake iko da su shi ne mala’ikan mahallaka, sunansa da Yahudanci Abadan, da Helenanci kuwa Afoliyon.
12 Bala’in farko ya wuce, ga kuma bala’i na biyu a nan a tafe.
13 Sa’an nan mala’ika na shida ya busa ƙahonsa, sai na ji wata murya daga zankayen nan huɗu na bagadin ƙona turare na zinariya a gaban Allah,
14 tana ce wa mala’ikan nan na shida mai ƙaho, “Ka saki mala’iku huɗun nan da suke a ɗaure a gabar babban kogin nan Yufiretis.”
15 Sai aka saki mala’ikun nan huɗu, waɗanda aka tanada saboda wannan sa’a, da wannan rana, da wannan wata, da wannan shekara, su kashe sulusin ‘yan adam.
16 Yawan rundunonin sojan doki kuwa, na ji adadinsu zambar dubu metan ne.
17 Ga kuwa yadda na ga dawakan a wahayin da aka yi mini, mahayansu suna saye da sulkuna, launinsu ja kamar wuta, da shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta, kawunan dawakan kuma kamar na zaki, wuta kuma da hayaƙi da farar wuta suna fita daga bakinsu.
18 Da waɗannan bala’i uku aka kashe sulusin ‘yan adam, wato, da wuta, da hayaƙi, da farar wuta da suke fita daga bakinsu.
19 Domin ikon dawakan nan na a bakinsu da a wutsiyarsu, wutsiyoyinsu kamar macizai suke, har da kawuna, da su ne suke azabtarwa.
20 Sauran ‘yan adam waɗanda bala’in nan bai kashe ba kuwa, ba su tuba sun rabu da abubuwan da suka yi da hannunsu ba, ba su kuma daina yin sujada ga aljannu, da gumakan zinariya, da na azurfa, da na tagulla, da na dutse, da na itace ba, waɗanda ba su iya gani, ko ji, ko tafiya,
21 ba su kuma tuba da kashe-kashenkai da suka yi ba, ko sihirinsu, ko fasikancinsu, ko kuma sace-sacensu.