Mutuwar Li’azaru
1 Wani mutum ne ya yi rashin lafiya, sunansa Li’azaru na Betanya, ƙauyen su Maryamu da ‘yar’uwarta Marta.
2 Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Li’azaru ba shi da lafiya, ita ce wadda ta shafa wa Ubangiji man ƙanshi, ta kuma shafe ƙafafunsa da gashinta.
3 To, ‘yan’uwan nan mata suka aika masa, suka ce, “Ya Ubangiji, ga shi, wanda kake ƙaunan nan ba shi da lafiya.”
4 Da Yesu ya ji haka ya ce, “Wannan rashin lafiya, ƙarshensa ba mutuwa ba ne, domin a ɗaukaka Allah ne, a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurinsa.”
5 Yesu kuwa na ƙaunar Marta da ‘yar’uwarta, da kuma Li’azaru.
6 To, da ya ji Li’azaru ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu.
7 Bayan haka ya ce wa almajiran, “Mu koma ƙasar Yahudiya.”
8 Almajiran suka ce masa, “Ya Shugaba, kwana kwanan nan fa Yahudawa suke neman jifanka, za ka sāke komawa can?”
9 Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa’a goma sha biyu ce yini ɗaya ba? Kowa yake tafiya da rana ba ya tuntuɓe, don yana ganin hasken duniyan nan.
10 Amma kowa yake tafiya da dare yakan yi tuntuɓe, don ba haske a gare shi!”
11 Ya faɗi haka, sa’an nan ya ƙara ce musu, “Amininmu Li’azaru ya yi barci, amma za ni in tashe shi.”
12 Sai almajiran suka ce masa, “Ya Ubangiji, in dai barci ne ya ɗauke shi, ai, zai warke.”
13 Alhali kuwa, Yesu zancen mutuwar Li’azaru yake, amma su sun ɗauka yana nufin barcin hutawa ne.
14 Sai Yesu ya gaya musu a fili, ya ce, “Li’azaru dai ya mutu.
15 Ina kuwa farin ciki da ba na nan, saboda ku domin ku ba da gaskiya. Amma mu dai je wurinsa.”
16 Sai Toma, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ya ce wa ‘yan’uwansa almajirai, “Mu ma mu tafi, mu mutu tare da shi.”
Yesu Shi Ne Tashin Matattu da Rai Kuma
17 Da Yesu ya isa, ya tarar Li’azaru, har ya kwana huɗu a kabari.
18 Betanya kuwa kusa da Urushalima take, misalin mil biyu.
19 Yahudawa da yawa sun zo su yi wa Marta da Maryamu ta’aziyyar ɗan’uwansu.
20 Da jin Yesu na zuwa, sai Marta ta je taryensa, Maryamu kuwa ta zauna a gida.
21 Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba.
22 Ko yanzu ma na sani kome ka roƙi Allah zai yi maka.”
23 Yesu ya ce mata, “Ɗan’uwanki zai tashi.”
24 Marta ta ce masa, “Na sani zai tashi a tashin matattu a ranar ƙarshe.”
25 Yesu ya ce mata, “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu.
26 Wanda kuwa yake raye, yake kuma gaskatawa da ni, ba zai mutu ba har abada. Kin gaskata wannan?”
27 Ta ce masa, “I, ya Ubangiji. Na gaskata kai ne Almasihu, Ɗan Allah, shi wannan mai zuwa duniya.”
Yesu Ya Yi Hawaye
28 Da ta faɗi haka, ta je ta kirawo ‘yar’uwa tata Maryamu, ta raɗa mata ta ce, “Ga Malam ya zo, yana kiranki.”
29 Ita kuwa da jin haka, ta yi maza ta tashi ta nufi wurinsa.
30 Yesu dai bai iso ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana wurin da Marta ta tarye shi.
31 Da Yahudawan da suke tare da ita a cikin gida, suna yi mata ta’aziyya, suka ga Maryamu ta yi maza ta tashi ta fita, suka bi ta, suna zaton za ta kabarin ne, ta yi kuka a can.
32 Da Maryamu ta iso inda Yesu yake, ta gan shi, sai ta faɗi a gabansa ta ce masa, “Ya Ubangiji, da kana nan da dan’uwana bai mutu ba.”
33 Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita su ma, suna kuka, sai ya nisa a ransa, ya yi juyayi gaya.
34 Ya kuma ce, “Ina kuka sa shi?” Suka ce masa, “Ya Ubangiji, zo ka gani.”
35 Sai Yesu ya yi hawaye.
36 Don haka Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”
37 Amma waɗansunsu suka ce, “Ashe, wanda ya buɗe wa makahon nan ido, ba zai iya hana wannan mutum mutuwa ba?”
Yesu Ya Ta da Li’azaru daga Matattu
38 Sai Yesu ya sāke nisawa a ransa, ya iso kabarin. Kabarin kuwa kogon dutse ne, da wani dutse kuma an rufe bakin.
39 Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.” Sai Marta, ‘yar’uwar mamacin, ta ce masa, “Ya Ubangiji, ai, yanzu ya yi ɗoyi, don yau kwanansa huɗu ke nan da mutuwa.”
40 Sai Yesu ya ce mata, “Ban gaya miki ba, in kin ba da gaskiya za ki ga ɗaukakar Allah?”
41 Sai suka kawar da dutsen. Yesu kuwa ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, na gode maka da ka saurare ni.
42 Ko dā ma na sani koyaushe kana saurarona, amma na faɗi haka ne saboda jama’ar da suke nan tsaitsaye, domin su gaskata kai ne ka aiko ni.”
43 Da ya faɗi haka ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Li’azaru fito!”
44 Sai mamacin ya fito, ƙafa da hannu a ɗaure da likkafani, fuska tasa kuma a naɗe da mayani. Yesu ya ce musu, “Ku kwance masa, ya tafi.”
An Kulla Shawara Gāba da Yesu
45 Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo wurin Maryamu, suka kuma ga abin da ya yi, suka gaskata da shi.
46 Amma waɗansunsu suka tafi wurin Farisiyawa, suka gaya musu abin da Yesu ya yi.
47 Don haka manyan firistoci da Farisiyawa suka tara ‘yan majalisa, suka ce, “Shin, me muke yi ne, har mutumin nan yake ta yin mu’ujizai da yawa haka?
48 In fa muka ƙyale shi kan haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma za su zo su karɓe ƙasarmu su ɗebe jama’armu.”
49 Amma ɗayansu, wai shi Kayafa, wanda yake shi ne babban firist a shekaran nan, ya ce musu, “Ku dai ba ku san kome ba.
50 Ba kwa lura, ai, ya fiye muku mutum ɗaya ya mutu saboda jama’a, da duk jama’a ta halaka.”
51 Ba da nufinsa ya faɗi haka ba, sai dai da yake shi ne babban firist a shekaran nan, ya yi annabci cewa, Yesu zai mutu saboda jama’a,
52 ba ma saboda jama’a kaɗai ba, har ma yă tattaro ‘ya’yan Allah da suke warwatse ko’ina su zama ɗaya.
53 Daga ran nan fa sai suka ƙulla su kashe shi.
54 Saboda haka, Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba, amma ya tashi daga wurin, ya tafi ƙasar da take a bakin jeji, ya shiga wani gari, mai suna Ifraimu. Nan ya zauna da almajiran.
55 Ana nan, Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya gabato, mutane da yawa daga ƙauye suka tafi Urushalima su tsarkake kansa kafin idin.
56 Suka yi ta neman Yesu, suna tsaitsaye a Haikali, suna ce wa juna, “Me kuka gani? Zai zo idin kuwa?”
57 Don dā ma, manyan firistoci da Farisiyawa sun yi umarni, cewa kowa ya san inda Yesu yake, ya zo ya faɗa, su kama shi.