Tashin Yesu daga Matattu
1 To, a ranar farko ta mako, Maryamu Magadaliya ta je kabarin da asuba, tun da sauran duhu, ta ga an kawar da dutsen daga kabarin.
2 Sai ta yiwo gudu wurin Bitrus da kuma almajirin nan da Yesu yake ƙauna, ta ce musu, “An ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuwa san inda aka sa shi ba.”
3 Sai Bitrus da almajirin nan suka fita suka doshi kabarin.
4 Duka biyu suka ruga a guje, amma almajirin nan ya tsere wa Bitrus, ya riga isa kabarin.
5 Yana duƙawa yana leƙa ciki, sai ya ga likkafanin lilin a ajiye, amma fa bai shiga ba.
6 Sa’an nan Bitrus ya zo a bayansa, ya kuwa shiga kabarin, ya ga likkafanin a ajiye,
7 mayanin kuma da yake kansa ba a ajiye tare da likkafanin yake ba, amma a naɗe shi kaɗai a waje ɗaya.
8 Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga, ya gani, ya kuma ba da gaskiya.
9 Don kafin lokacin nan ba su fahimci Nassin nan ba, cewa lalle ne yă tashi daga matattu.
10 Sai almajiran suka koma gida.
Yesu Ya Bayyana ga Maryamu Magadaliya
11 Maryamu kuwa tana tsaye a bakin kabarin daga waje, tana kuka. Tana cikin kuka sai ta duƙa, ta leƙa kabarin,
12 sai ta ga mala’iku biyu saye da fararen tufafi a zaune inda dā gawar Yesu take, ɗaga wajen kai, ɗaya kuwa wajen ƙafafu.
13 Suka ce mata, “Uwargida, don me kike kuka?” Ta ce musu, “Ai, an ɗauke Ubangijina, ban kuwa san inda aka sa shi ba.”
14 Da ta faɗi haka sai ta juya ta ga Yesu tsaye, amma ba ta gane Yesu ne ba.
15 Yesu ya ce mata, “Uwargida, don me kike kuka? Wa kuma kike nema?” Saboda kuma ta zaci shi ne mai aikin lambun, ta ce masa, “Maigida, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka sa shi mana, ni kuwa in ɗauke shi.”
16 Yesu ya ce mata, “Maryamu!” Sai ta juya ta ce masa da Yahudanci, “Rabboni!” wato Malam.
17 Yesu ya ce mata, “Kada ki riƙe ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna. Sai dai ki tafi wurin ‘yan’uwana ki ce musu ina hawa wurin Ubana kuma Ubanku, Allahna kuma Allahnku.”
18 Sai Maryamu Magadaliya ta je ta ce wa almajiran, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma ce shi ya faɗa mata waɗannan abubuwa.
Yesu Ya Bayyana ga Almajiransa
19 A ran nan da magariba, ranar farko ta mako, ƙofofin ɗakin da almajiran suke ciki na kulle don tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce musu, “Salama alaikun!”
20 Da ya faɗi haka, ya nuna musu hannuwansa da kwiɓinsa. Sai almajiran suka yi farin ciki da ganin Ubangiji.
21 Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama alaikun! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma na aike ku.”
22 Da ya faɗi haka ya busa musu numfashinsa, ya ce musu, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki.
23 Duk waɗanda kuka gafarta wa zunubansu, an gafarta musu ke nan. Duk waɗanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta ba ke nan.”
Rashin Bangaskiyar Toma
24 Toma kuwa, ɗaya daga cikin goma sha biyun nan, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ba ya nan tare da su sa’ad da Yesu ya zo.
25 Sai sauran almajiran suka ce masa, “Mun ga Ubangiji.” Amma ya ce musu, “In ban ga gurbin ƙusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsata a gurbin ƙusoshin, in kuma sa hannuna a kwiɓinsa ba, ba zan ba da gaskiya ba.”
26 Bayan kwana takwas har wa yau almajiransa na cikin gidan, Toma ma yana nan tare da su, ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce, “Salama alaikun.”
27 Sa’an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsanka nan, ka ji hannuwana. Miƙo hannunka kuma ka sa a kwiɓina. Kada ka zama marar ba da gaskiya, sai dai mai ba da gaskiya.”
28 Toma ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangijina Allahna kuma!”
29 Sai Yesu ya ce masa, “Wato saboda ka gan ni ka ba da gaskiya? Albarka tā tabbata ga waɗanda ba su gani ba, amma kuwa suka ba da gaskiya.”
Manufar Littafin Nan
30 Yesu ya yi waɗansu mu’ujizai da yawa dabam dabam a gaban almajiran, waɗanda ba a rubuta a littafin nan ba.
31 Amma an rubuta waɗannan ne, domin ku ba da gaskiya Yesu shi ne Almasihu, Ɗan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai a cikin sunansa.