Fāra ta Zama Musu Alamar Ranar Ubangiji
1 Ku busa ƙaho, ku yi gangami,
A cikin Sihiyona, tsattsarkan
dutsen Allah!
Duk mutanen ƙasar za su yi rawar
jiki,
Domin ranar Ubangiji tana zuwa, ta
yi kusa.
2 Za ta zama rana ce mai duhu
dulum,
Ranar gizagizai ce baƙi ƙirin.
Runduna mai ƙarfi tana tasowa,
Kamar ketowar hasken safiya bisa
tsaunuka.
Faufau ba a taɓa ganin irinta ba,
Ba kuwa za a sāke ganin irinta ba.
3 Tana cinye shuke-shuke kamar wuta,
Ƙasa kamar gonar Adnin take kafin
ta zo,
Amma a bayanta ta zama hamada,
Ba abin da ya tsere mata.
4 Kamar doki take,
Tana gudu kamar dokin yaƙi.
5 Motsin tsallenta a kan duwatsu
kamar Motsin karusa ne.
Kamar kuma amon wutar da take cin
tattaka.
Kamar runduna mai ƙarfi wadda ta
ja dāgar yaƙi.
6 Da zuwanta mutane sukan firgita,
Dukan fuskoki sukan ɓaci.
7 Takan auka kamar mayaƙa,
Takan hau garu kamar sojoji,
Takan yi tafiya,
Kowa ta miƙe sosai inda ta sa
gaba,
Ba ta kaucewa.
8 Ba ta hawan hanyar juna,
Kowa tana bin hanyarta.
Takan kutsa cikin abokan gāba, ba a
iya tsai da ita.
9 Takan ruga cikin birni,
Takan hau garu a guje,
Takan hau gidaje,
Takan shiga ta tagogi kamar ɓarawo.
10 Duniya takan girgiza saboda ita,
Sammai sukan yi rawar jiki.
Rana da wata sukan duhunta,
Taurari kuwa sukan daina
haskakawa.
11 Ubangiji yakan umarci rundunarsa,
Rundunarsa mai cika umarninsa
babba ce, mai ƙarfi,
Gama ranar Ubangiji babba ce mai
banrazana.
Wa zai iya daurewa da ita?
Jinƙan Ubangiji
12 “Koyanzu,” in ji Ubangiji,
“Ku juyo wurina da zuciya ɗaya,
Da azumi, da kuka, da makoki,
13 Ku kyakkece zuciyarku, ba tufafinku
kaɗai ba.”
Ku komo wurin Ubangiji Allahnku.
Gama shi mai alheri ne, mai jinƙai,
Mai jinkirin fushi ne, mai yawan
ƙauna,
Yakan tsai da hukunci.
14 Wa ya sani ko Ubangiji Allahnmu zai
sāke nufinsa,
Ya sa mana albarka,
Har mu miƙa masa hadaya ta gari da
ta sha?
15 Ku busa ƙaho a Sihiyona,
Ku sa a yi azumi,
Ku kira muhimmin taro.
16 Ku tattara jama’a wuri ɗaya,
Ku tsarkake taron jama’a,
Ku tattara dattawa da yara,
Har da jarirai masu shan mama.
Ku sa ango ya fito daga cikin
turakarsa,
Amarya kuma ta fito daga cikin
ɗakinta.
17 Sai firistoci masu hidimar Ubangiji,
Su yi kuka a tsakanin shirayi da
bagade,
Su ce, “Ya Ubangiji, ka ceci
jama’arka,
Kada ka bar gādonka ya zama abin
zargi
Da abin ba’a a tsakiyar al’ummai.
Don kada al’ummai su ce,
‘Ina Allahnsu?’ ”
18 Sai Ubangiji ya ji kishin ƙasarsa,
Ya kuma ji ƙan mutanensa.
19 Sa’an nan ya ce musu,
“Ga shi, zan ba ku hatsi da ruwan
inabi, da mai,
Za ku ƙoshi.
Ba zan sa ku ƙara zama abin zargi ga
al’ummai ba.
20 Zan kawar muku da waɗanda suka
zo daga arewa,
Zan kori waɗansunsu zuwa cikin
hamada.
Zan kori sahunsu na gaba zuwa cikin
Tekun Gishiri,
Zan kori sahunsu na baya, zuwa
cikin Bahar Rum.
Gawawwakinsu za su yi ɗoyi.
Zan yi musu haka saboda dukan abin
da suka yi muku.”
21 Kada ki ji tsoro, ya ƙasa,
Ki yi farin ciki, ki yi murna,
Gama Ubangiji ne ya yi waɗannan
manyan al’amura.
22 Kada ku ji tsoro, ku dabbobin
saura,
Gama wuraren kiwo a jeji sun yi kore
shar.
Itatuwa suna ta yin ‘ya’ya,
Itacen ɓaure da kurangar inabi suna
ta yin ‘ya’ya sosai.
23 Ya ku mutanen Sihiyona, ku yi
murna,
Ku yi farin ciki da Ubangiji
Allahnku,
Gama ya ba ku ruwan farko
Domin shaidar gafarar da ya yi
muku,
Ya kwararo muku da ruwan farko da
na ƙarshe da yawa kamar dā.
24 Masussukai za su cika da hatsi,
Wuraren matse ruwan inabi za su
malala da ruwan inabi.
25 “Zan mayar muku da abin da kuka
yi hasararsa
A shekarun da fara ta cinye
amfaninku,
Wato ɗango da fara mai gaigayewa,
da mai cinyewa,
Su ne babbar rundunata wadda na
aiko muku.
26 Yanzu za ku ci abinci a wadace ku
ƙoshi,
Za ku yabi sunan Ubangiji
Allahnku,
Wanda ya yi muku abubuwa masu
banmamaki,
Ba kuma za a ƙara kunyatar da
mutanena ba.
27 Ku mutanen Isra’ila, za ku sani ina
cikinku,
Ni ne kuwa Ubangiji Allahnku, ba
wani kuma,
Ba kuma za a ƙara kunyatar da
mutanena ba.”
Za a Ba da Ruhun Allah
28 “Bayan wannan zan zubo Ruhuna a
kan jama’a duka,
‘Ya’yanku mata da maza za su iyar
da saƙona,
Tsofaffinku kuwa za su yi mafarkai,
Samarinku za su ga wahayi da yawa.
29 A lokacin zan zubo Ruhuna,
Har a kan barori mata da maza.
30 “Zan yi faɗakarwa a kan wannan
rana
A sararin sama da a duniya.
Za a ga jini, da wuta, da murtukewar
hayaƙi,
31 Rana za ta duhunta,
Wata zai zama ja wur kamar jini,
Kafin isowar babbar ranan nan mai
bantsoro ta Ubangiji.
32 Amma dukan waɗanda suka nemi
Ubangiji za su tsira.
Kamar yadda Ubangiji ya ce,
Akwai waɗanda suke a Dutsen
Sihiyona da Urushalima
Da za su tsira,
Waɗannan da Ubangiji ya zaɓa za su
tsira.”