Addu’ar Yunusa ta Godiya
1 Sai Yunusa ya yi addu’a ga Ubangiji Allah a cikin cikin kifin,
2 ya ce,
“A cikin wahalata na yi kira gare ka,
ya Ubangiji,
Ka a kuwa amsa mini.
Daga can cikin lahira na yi kira,
Ka kuwa ji muryata.
3 Ka jefa ni cikin zurfi,
Can cikin tsakiyar teku,
Inda igiyoyin ruwa suka kewaye ni,
Kumfa da raƙuman ruwanka suka
bi ta kaina.
4 Na ce, an kore ni daga wurinka,
Duk da haka zan sāke ganin
Haikalinka mai tsarki.
5 Ruwa ya sha kaina,
Tekun ta rufe ni ɗungum.
Tsire-tsiren teku suka naɗe kaina.
6 Na tafi can ƙasa ƙarƙashin tussan
duwatsu.
Ƙasar da ƙofarta take rufe har abada,
Amma ka fitar da ni daga cikin
ramin, ya Ubangiji Allahna.
7 Sa’ad da na ji raina yana rabuwa da
ni,
Sai na tuna da kai, ya Ubangiji.
Addu’ata kuwa ta kai gare ka a
Haikalinka tsattsarka.
8 Su waɗanda suke yin sujada ga gumaka
marasa amfani
Sun daina yi maka biyayya.
9 Amma ni zan raira yabbai gare ka,
Zan miƙa maka sadaka,
Zan cika wa’adin da na yi.
Ceto daga wurin Ubangiji yake.”
10 Ubangiji kuwa ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunusa a gaɓar teku.