Tuban Ninebawa
1 Ubangiji kuma ya sāke ce wa Yunusa,
2 “Ka tashi ka tafi Nineba, babban birnin nan, ka yi musu shelar saƙon da zan faɗa maka.”
3 Sai Yunusa ya tashi ya tafi Nineba kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa. Nineba kuwa babban birni ne. Zai kai mutum tafiyar kwana uku kafin yă ƙure birnin.
4 Sai Yunusa ya kama tafiya yana ratsa birnin, da ya yi tafiyar yini guda, sai ya yi shela ya ce, “Nan da kwana arba’in za a hallaka Nineba.”
5 Sai mutanen Nineba suka gaskata Allah, suka tsai da shawara, cewa kowa da kowa ya yi azumi. Dukan mutane kuwa babba da yaro, suka sa tufafin makoki.
6 Sa’ad da Sarkin Nineba ya ji labarin, sai ya sauka daga kursiyinsa, ya tuɓe rigarsa, ya sa rigar makoki, ya zauna cikin toka.
7 Sai ya aika wa mutanen Nineba da sanarwa cewa, “Wannan doka ce daga sarki da majalisarsa. Kada kowa ya ci wani abu, mutane, da shanu, da tumaki, da awaki duka, kada kowa ya ci, ko ya sha ruwa.
8 Sai dukan mutane da dabbobi su sa tufafin makoki. Kowa ya roƙi Allah da gaske, kowa kuma ya bar mugayen ayyukan da yake yi.
9 Kila Allah zai dakatar da nufinsa, fushinsa ya huce, ya bar mu mu tsira daga mutuwa!”
10 Allah kuwa ya ga abin da suka yi, ya ga yadda suka bar mugayen ayyukansu, sai ya dakatar da nufinsa, bai hallaka su ba.