YUSH 10

1 Isra’ila kurangar inabi ce mai bansha’awa

Wadda yake ba da ‘ya’ya da yawa.

Ƙara yawan arzikinsu,

Ƙara gina bagadansu.

Ƙara yawan wadatar ƙasarsu.

Ƙara kyautata ginshiƙansu.

2 Zuciyarsu ta munafunci ce,

Yanzu tilas za su ɗauki hakkin laifinsu,

Ubangiji zai farfashe bagadansu da ginshiƙansu.

3 Gama yanzu za su ce,

“Ba mu da sarki,

Domin ba mu ji tsoron Ubangiji ba.

Amma me sarki zai yi mana?”

4 Surutai kawai suke yi,

Suna yin alkawaran ƙarya,

Don haka hukunci zai zaburo kamar muguwar ciyawa mai dafi a kunyoyin gona.

5 Mazaunan Samariya suna rawar jiki

Domin ɗan maraƙin Bet-awen,

Mutane za su yi makoki dominsa,

Firistoci matsafa, za su yi kururuwa dominsa,

Da kuma darajarsa wadda ta rabu da shi.

6 Za a kai ɗan maraƙin a Assuriya

Don a biya wa sarki haraji.

Za a kunyatar da Ifraimu,

Isra’ila kuwa za ta ji kunya saboda shawararta.

7 Sarakunan Samariya za su ɓace,

Kamar kumfa a bisa ruwa.

8 Za a hallaka masujadan tuddai na Awen inda Isra’ila suke yin zunubi,

Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma a bagadansu.

Za su ce wa manyan duwatsu, “Ku rufe mu!”

Su ce wa tuddai, “Ku faɗo bisa kanmu!”

9 Ubangiji ya ce, “Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra’ila!

Tun daga wancan lokaci kuka yi ta ci gaba.

Ashe, yaƙi ba zai tarshe su a Gibeya ba?

10 Zan fāɗa wa waɗannan mutane masu zunubi, in hukunta su.

Za a tattara al’ummai, su yi gāba da su,

Za a hukunta su saboda yawan zunubansu.

11 “Ifraimu horarriyar karsana ce,

Wadda yake jin daɗin yin sussuka,

Amma na sa wa kyakkyawan wuyanta karkiya,

Na sa Yahuza ta ja garmar noma,

Yakubu kuwa za ta ja garmar bajiya.

12 Ku shuka wa kanku adalci,

Ku girbe albarkun ƙauna,

Ku yi kautun saurukanku,

Gama lokacin neman Ubangiji ya yi,

Domin ya zo, ya koya muku adalci.

13 Kun shuka mugunta,

Kun girbe rashin adalci,

Kun ci amfanin ƙarya.

“Da yake dogara ga hanyarku da ɗumbun sojojinku,

14 Domin haka hayaniyar yaƙi za ta tashi a tsakanin jama’arku.

Dukan kagaranku za a hallaka su.

Kamar yadda Shalmanesar ya hallaka Bet-arbel a ranar yaƙi.

An fyaɗa uwaye da ‘ya’yansu a ƙasa.

15 Haka za a yi muku, ya mutanen Betel, saboda yawan muguntarku.

Da asuba za a datse Sarkin Isra’ila.”