YUSH 5

Hukunci a kan Riddar Isra’ilawa

1 “Ku ji wannan, ya ku firistoci!

Ku saurara, ya mutanen Isra’ila!

Ku kasa kunne, ya gidan sarki!

Gama za a yi muku hukunci,

Domin kun zama tarko a Mizfa,

Da ragar da aka shimfiɗa a bisa Tabor.

2 Sun tayar, sun yi zurfi cikin zunubi,

Zan hore su duka.

3 Na san Ifraimu, Isra’ila kuma ba a ɓoye take a gare ni ba.

Gama Ifraimu ta yi aikin karuwanci,

Isra’ila kuma ta ƙazantu.

4 “Ayyukansu ba su bar su

Su koma wurin Allahnsu ba,

Gama halin karuwanci yana cikinsu,

Don haka kuma ba su san Ubangiji ba.

5 Girmankan mutanen Isra’ila yana ba da shaida a kansu.

Mutanen Ifraimu za su yi tuntuɓe cikin laifinsu.

Mutanen Yahuza kuma za su yi tuntuɓe tare da su.

6 Da garkunan tumaki da na awaki, da na shanunsu

Za su tafi neman Ubangiji,

Amma ba za su same shi ba,

Gama ya rabu da su.

7 Sun ci amanar Ubangiji.

Su haifi shegu.

Yanzu amaryar wata za ta cinye su da gonakinsu.

Yaƙi tsakanin Mutanen Yahuza da na Isra’ila

8 “Ku busa ƙaho cikin Gibeya,

Ku busa kakaki cikin Rama,

Ku yi gangami cikin Bet-awen,

Ku yi rawar yaƙi, ya ku Biliyaminu!

9 Ifraimu za ta zama kango a ranar hukunci.

A kabilan Isra’ila na sanar da abin da zai faru, ba makawa.

10 “Shugabannin Yahuza sun zama kamar masu cin iyaka,

Zan zubo musu da fushina kamar ruwa.

11 An danne Ifraimu, shari’a ta murƙushe ta,

Domin ta ƙudura ta bi banza.

12 Domin haka na zama kamar asu ga Ifraimu,

Kamar ruɓa ga mutanen Yahuza.

13 “Sa’ad da Ifraimu ta ga ciwonta,

Yahuza kuma ta ga rauninta,

Sai Ifraimu ta aika zuwa Assuriya,

Wurin babban sarki.

Amman ba zai iya warkar da ciwonki, ko rauninki ba.

14 Zan zama kamar zaki ga Ifraimu,

Kamar sagarin zaki ga mutanen Yahuza.

Ni kaina zan yayyage, in yi tafiyata.

Zan ɗauka, in tafi, ba wanda zai yi ceto.

Isra’ila Ta Yi Tuban Muzuru

15 “Zan koma wurin zamana

Sai lokacin da suka yarda sun yi zunubi, su neme ni.

A cikin ƙuncinsu za su neme ni.”