Addu’ar Wanda Yake Shan Wahala
1 Ka ji addu’ata, ya Ubangiji,
Ka ji kukana na neman taimako!
2 Kada ka ɓoye mini sa’ad da nake shan wahala!
Ka ji ni, ka amsa mini da sauri sa’ad da na yi kira!
3 Raina ya ɓace kamar hayaƙi,
Jikina yana ƙuna kamar wuta.
4 An tattake ni kamar busasshiyar ciyarwa,
Ba ni da marmarin cin abinci.
5 Ina nishi da ƙarfi,
Ba abin da ya ragu gare ni,
In banda ƙashi da fata.
6 Ni kamar tsuntsu nake cikin hamada,
Kamar mujiya a kufai.
7 Kwana nake ba barci,
Na zama kamar tsuntsun da yake fama da kewa
A bisa kan ɗaki.
8 Maƙiyana suna cin mutuncina dukan yini.
Waɗanda suke mini ba’a,
Suna la’antarwa da sunana.
9 Toka ce abincina,
Hawayena kuwa sun gauraya da abin shana,
10 Sabili da fushinka da hasalarka.
Ka ɗauke ni, ka jefar da ni.
11 Raina kamar inuwar maraice yake,
Kamar busasshiyar ciyawa nake.
12 Amma kai, ya Ubangiji, sarki ne kai har abada,
Dukan zamanai masu zuwa za su tuna da kai.
13 Za ka tashi ka ji tausayin Sihiyona,
Lokaci ya yi da za ka yi mata jinƙai,
Wannan shi ne lokacin!
14 Bayinka suna ƙaunarta,
Ko da yake an hallakar da ita,
Suna jin tausayinta,
Ko da yake ta zama kufai.
15 Sauran al’umma za su ji tsoron Ubangiji,
Dukan sarakunan duniya za su ji tsoron ikonsa.
16 Sa’ad da Ubangiji ya sāke gina Sihiyona
Zai bayyana girmansa.
17 Zai saurari jama’arsa wadda ya rabu da ita,
Zai kuwa ji addu’arta.
18 Ku rubuta abin da Ubangiji ya aikata don zamani mai zuwa,
Don waɗanda ba a haife su ba tukuna,
Su ma su yabe shi.
19 Ubangiji ya duba ƙasa
Daga Sama, tsattsarkan wurinsa,
Daga Sama ya dubi duniya,
20 Don ya ji nishin ɗaurarru,
Don ya saki waɗanda aka yanke musu hukuncin kisa.
21 Saboda wannan mutane za su yi shelar sunan Ubangiji a Sihiyona,
Za su yi masa godiya a Urushalima,
22 Sa’ad da sauran al’umma da mulkoki suka taru
Don su yi wa Ubangiji sujada.
23 Tun ina ƙaramin yaro Ubangiji ya sa na rasa ƙarfi,
Ya gajerta kwanakina.
24 Ya Allahna, kada ka ɗauke ni a yanzu,
Tun da yake ban tsufa ba tukuna!
Ya Ubangiji har abada kake.
25 Ka halicci duniya tun tuntuni,
Da ikonka ne ka yi sammai.
26 Su za su ɓace duka, amma kai za ka dawwama,
Za su ƙare kamar yadda tufafi suke ƙarewa,
Za ka sāke su kamar tufafi, za su kuwa ɓace.
27 Amma kai, kana yadda kake kullayaumin,
Har abada kake.
28 ‘Ya’yanmu za su yi zaman lafiya,
Zuriyarsu kuma za su zauna cikin kiyayewarka kullayaumin.