Ubangiji Ya Ba Sarkin da Ya Zaɓa Iko
1 Ubangiji ya ce wa Mai Girma, Sarkina,
“Zauna nan a damana,
Har in sa maƙiyanka a ƙarƙashin sawayenka.”
2 Tun daga Sihiyona Ubangiji zai faɗaɗa sarautarka, ya ce,
“Ka yi mulki bisa maƙiyanka.”
3 A ranar da za ka yi yaƙi da maƙiyanka,
Jama’arka za su kawo maka gudunmawa don kansu.
Kamar yadda raɓa take da sassafe,
Haka samarinka za su zo wurinka a tsarkakan tsaunuka.
4 Ubangiji ya yi muhimmin alkawari,
Ba kuwa zai fasa ba!
“Za ka zama firist har abada
Bisa ga tsabi’ar Malkisadik firist.”
5 Ubangiji yana damanka,
Zai kori sarakuna a ranar da ya husata.
6 Zai shara’anta wa dukan sauran al’umma,
Ya rufe fagen fama da gawawwaki,
Zai kori sarakunan duk duniya.
7 Sarkin zai sha ruwan rafin da yake kan hanya,
Ya wartsake ya sami ƙarfi.
Zai yi tsayawar nasara.