Kiyayewar Ubangiji ga Jama’arsa
1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
Zan yi wa Ubangiji godiya da zuciya ɗaya,
A cikin taron jama’arsa.
2 Abubuwan banmamaki ne Ubangiji yake aikatawa!
Duk waɗanda suke murna da su
Suna so su fahimce su.
3 Dukan abin da yake yi,
Cike yake da girma da ɗaukaka,
Adalcinsa har abada ne.
4 Ubangiji ba zai bar mu mu manta da ayyukansa masu banmamaki ba,
Shi mai alheri ne, mai jinƙai kuma.
5 Yakan tanada wa masu tsoronsa abinci,
Bai taɓa mantawa da alkawarinsa ba.
6 Ya nuna ikonsa ga jama’arsa
Saboda ya ba su ƙasashen baƙi.
7 Iyakar abin da yake yi duka, da aminci da adalci ne.
Dukan umarnansa, abin dogara ne.
8 Sukan tabbata har abada,
Da gaskiya da adalci aka ba da su.
9 Ya kawo wa jama’arsa ceto,
Ya kuma yi musu madawwamin alkawari.
Mai Tsarki ne shi, Maɗaukaki!
10 Hanyar samun hikima, ita ce tsoron Ubangiji,
Yakan ba da kyakkyawar ganewa
Ga dukan waɗanda suke bin umarnansa,
Sai ku yabe shi har abada!