ZAB 115

Allah Mai Gaskiya Makaɗaici

1 A gare ka kaɗai, ya Ubangiji,

A gare ka kaɗai, ba a gare mu ba,

Dole a girmama ka,

Sabili da madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.

2 Me ya sa sauran al’umma suke tambayarmu,

“Ina Allahnku?”

3 Allahnmu yana Sama,

Yana aikata yadda yake so.

4 Amma nasu alloli na azurfa da zinariya ne,

Da hannu aka siffata su.

5 Suna da baki, amma ba sa magana,

Suna da idanu, amma ba sa gani.

6 Suna da kunnuwa, amma ba sa ji,

Suna da hanci, amma ba sa jin ƙanshi.

7 Suna da hannuwa, amma ba sa iya riƙon kome,

Suna da ƙafafu, amma ba sa iya tafiya.

Ba su da murya sam.

8 Ka sa waɗanda suka yi su,

Da dukan masu dogara gare su,

Su zama kamar gumakan da suka yi!

9 Ku dogara ga Ubangiji, ya ku jama’ar Isra’ila!

Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.

10 Ku dogara ga Ubangiji, ya ku firistoci na Allah!

Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.

11 Ku dogara ga Ubangiji, dukanku waɗanda kuke tsoronsa!

Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.

12 Ubangiji yana tuna da mu, zai kuwa sa mana albarka,

Zai sa wa jama’ar Isra’ila albarka,

Da dukan firistoci na Allah.

13 Zai sa wa dukan waɗanda suke tsoronsa albarka.

Babba da yaro.

14 Ubangiji ya ba ku ‘ya’ya,

Ku da zuriyarku.

15 Ubangiji, wanda ya yi sama da ƙasa

Ya sa muku albarka!

16 Samaniya ta Ubangiji ce kaɗai,

Amma ya ba mutane duniya.

17 Matacce ba ya yabon Ubangiji,

Ko wanda ya gangara zuwa cikin kabari.

18 Amma mu da muke rayayyu, za mu yi masa godiya.

A yanzu da har abada.

Yabo ya tabbata ga Ubangiji!