Godiya domin Alherin Ubangiji
1 Da zuciya ɗaya nake gode maka, ya Ubangiji,
Ina raira waƙar yabonka a gaban alloli.
2 Na durƙusa a gaban tsattsarkan Haikalinka
Ina yabon sunanka.
Sabili da madawwamiyar ƙaunarka da amincinka,
Saboda ka nuna ɗaukakarka da umarnanka.
3 Ka amsa mini sa’ad da na yi kira gare ka,
Da ƙarfinka ka ƙarfafa ni.
4 Dukan sarakunan duniyar nan za su yabe ka, ya Ubangiji,
Gama sun riga sun ji alkawaranka.
5 Za su raira waƙa a kan abin da Ubangiji ya yi,
Za su raira waƙa kuma a kan ɗaukakarsa mai girma.
6 Ko da yake Ubangiji yana can Sama,
Duk da haka yana kulawa da masu kaɗaici.
Masu girmankai kuwa ba za su iya ɓoye kansu daga gare shi ba.
7 Ko lokacin da nake tsakiyar wahala,
Za ka kiyaye ni lafiya,
Ka yi gāba da abokan gābana, waɗanda suka husata,
Za ka kuwa cece ni da ikonka.
8 Za ka aikata kowane abu da ka alkawarta mini,
Ya Ubangiji, ƙaunarka madawwamiya ce har abada.
Ka cikasa aikin da ka fara.