Yabon Allah Mai Ceto
1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
Ka yabi Ubanigji, ya raina!
2 Zan yabe shi muddin raina.
Zan raira waƙa ga Allahna dukan kwanakina.
3 Kada ka dogara ga shugabanni,
Ko kowane mutum da ba zai iya cetonka ba.
4 Sa’ad da suka mutu sai su koma turɓaya,
A wannan rana dukan shirye-shiryensu sun ƙare.
5 Mai farin ciki ne mutumin da Allah na Yakubu ne yake taimakonsa,
Yana kuma dogara ga Ubangiji Allahnsa,
6 Wanda ya halicci sama, da duniya, da teku,
Da dukan abin da yake cikinsu.
Kullum yakan cika alkawaransa.
7 A yanke shari’arsa yakan ba wanda aka zalunta gaskiya.
Yana ba da abinci ga mayunwata.
Ubangiji yakan kuɓutar da ɗaurarru.
8 Yakan ba makafi ganin gari.
Yakan ɗaukaka waɗanda aka wulakanta.
Yana ƙaunar jama’arsa, adalai.
9 Yakan kiyaye baƙi waɗanda suke zaune a ƙasar.
Yakan taimaki gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu.
Yakan lalatar da dabarun mugaye.
10 Ubangiji Sarki ne har abada!
Ya Sihiyona, Allahnki zai yi mulki har dukan zamanai!
Yabo Ya tabbata ga Ubangiji!