Allah ne Mai Shari’a
1 Allah Maɗaukaki, Ubangiji, ya yi magana,
Yana kiran dukan duniya, daga gabas zuwa yamma.
2 Allah yana haskakawa daga Sihiyona,
Da cikar jamalin Sihiyona.
3 Allahnmu ya zo, ba a ɓoye yake ba,
Wuta mai cinyewa na tafe a gabansa,
Babban hadiri kuwa na kewaye da shi.
4 Ya kira sammai da duniya su zama shaidu,
Su ga yadda yake shara’anta jama’arsa.
5 Ya ce, “Ku tattaro mini amintattuna,
Waɗanda suka cika alkawarin da yake tsakanina da su,
Ta wurin miƙa hadaya.”
6 Sammai suna shelar adalcin Allah,
Domin shi yake yin shari’a!
7 “Ku ji, ya ku jama’ata, zan kuwa yi magana,
Zan ba da shaida gāba da ku, ya Isra’ila.
Ni ne Allah, Allahnku.
8 Ban tsauta muku saboda hadayunku ba,
Ko saboda hadayu na ƙonawa da kuke ta miƙa mini kullum.
9 Ba na bukatar bijimai daga gonakinku,
Ko awaki daga garkunanku.
10 Gama namomin jeji nawa ne,
Dubban shanu da suke kan tuddai kuma nawa ne.
11 Dukan tsuntsayen da suke tashi a sararin sama nawa ne,
Da dukan masu rai da suke ƙasa.
12 “Da ina jin yunwa ba sai na faɗa muku ba,
Gama da duniya da dukan abin da yake cikinta nawa ne.
13 Nakan ci naman bijimai ne?
Ko nakan sha jinin awaki?
14 Bari ku miƙa wa Allah hadayarku ta godiya,
Ku ba Mai Iko Dukka, dukan hadayun da kuka alkawarta.
15 Ku yi kira gare ni sa’ad da wahala ta zo,
Zan cece ku,
Ku kuwa za ku yabe ni.”
16 Amma Allah ya ce wa mugaye,
“Don me za ku haddace umarnaina?
Don me za ku yi magana a kan alkawaraina?
17 Kun ƙi in tsauta muku,
Kun yi watsi da umarnaina.
18 Sa’ad da kuka ga ɓarawo kukan yi abuta da shi.
Kuna haɗa kai da mazinata.
19 “Kullum a shirye kuke ku hurta mugunta,
Ba ku jin nauyin faɗar ƙarya.
20 A shirye kuke ku sari ‘yan’uwanku,
Ku sa musu laifi.
21 Kun aikata waɗannan duka, ni kuwa ban ce kome ba,
Saboda haka kuka zaci ni kamar ku nake.
Amma yanzu zan tsauta muku,
In bayyana muku al’amarin a fili.
22 “Ku ji wannan ku da kuke ƙyale ni,
In ba haka ba zan hallaka ku,
Ba wanda zai cece ku.
23 Wanda yake yin godiya a sa’ad da yake miƙa hadayarsa, yana girmama ni,
Da wanda yake yi mini biyayya kuma, zan nuna masa cetona.”