Hukuncin Allah da Alherinsa
1 Me ya sa kake fariya da muguntarka,
Ya kai, babban mutum?
Ƙaunar Allah tana nan a koyaushe.
2 Kana shirya maƙarƙashiya don ka lalatar da waɗansu,
Harshenka kamar aska mai kaifi yake.
Kana ƙirƙiro ƙarairayi kullum.
3 Kana ƙaunar mugunta fiye da nagarta,
Kana kuwa ƙaunar faɗar ƙarya fiye da gaskiya.
4 Kana jin daɗin cutar mutane da maganganunka,
Ya kai, maƙaryaci!
5 Don haka Allah zai ɓata ka har abada,
Zai kama ka, yă jawo ka daga alfarwarka,
Zai kawar da kai daga ƙasar masu rai.
6 Adalai za su ga wannan, su ji tsoro,
Za su yi maka dariya, su ce,
7 “Duba, ga mutumin da bai dogara ga Allah
Don ya sami zaman lafiyarsa ba.
A maimakon haka, sai ya dogara ga wadatarsa.
Yana neman zaman lafiyarsa ta wurin muguntarsa.”
8 Amma ni, kamar itacen zaitun nake, wanda yake girma kusa da Haikalin Allah,
Ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa har abada abadin.
9 Zan gode maka, ya Ubangiji,
Saboda abin da ka aikata.
Zan dogara gare ka,
Sa’ad da nake sujada tare da jama’arka,
Domin kai mai alheri ne.