Addu’ar Neman Kuɓuta daga Tsanani
1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi jinƙai,
Gama na zo gare ka neman tsira.
Zan sami kāriya a ƙarƙashin fikafikanka,
Sai dukan hatsari ya wuce.
2 Zan yi kira ga Allah, Maɗaukaki,
Zan yi kira ga Allah, mai biyan dukan bukatata.
3 Daga sammai Allah zai amsa mini,
Zai kori waɗanda suka tasar mini,
Allah zai nuna mini madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa.
4 Raina yana tsakiyar zakoki,
Na kwanta a tsakiyar waɗanda suka yi niyyar cinye mutane.
Haƙoransu kamar māsu da kibau suke,
Harsunansu masu kaifi ne kamar takobi.
5 Ka bayyana girmanka ya Allah, a sararin sama,
Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!
6 Maƙiyana sun kafa tarko don su kama ni,
Damuwa ta fi ƙarfina.
Sun yi wushefe a kan hanyata,
Amma su da kansu suka fāɗa a ciki.
7 A shirye nake, ya Allah,
Na shirya sosai!
Zan raira waƙoƙi in yabe ka!
8 Ka farka, ya raina!
Ku farka, molona da garayata!
Zan sa rana ta farka!
9 Zan gode maka a cikin sauran al’umma, ya Ubangiji!
Zan yabe ka a cikin jama’a!
10 Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har sammai,
Amincinka kuma har sararin sammai.
11 Ka bayyana girmanka, ya Allah, a sararin sama,
Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!