Addu’a domin A Hukunta Mugaye
1 Hakika za ku yanka daidai, ku manya?
Za ku shara’anta wa mutane daidai?
2 A’a, tunanin muguntar da za ku aikata kaɗai kuke yi,
Kuna aikata laifofin ta da hargitsi a ƙasar.
3 Mugaye, laifi suke yi dukan kwanakinsu,
Tun daga ranar da aka haife su suke ta faɗar ƙarya.
4 Cike suke da dafi kamar macizai,
Sukan toshe kunnuwansu kamar kuraman gamsheƙa,
5 Wanda ba ya jin muryar gardi,
Ko kuma waƙar gwanin sihiri.
6 Ka kakkarya haƙoransu, ya Allah,
Ka ciccire fiƙoƙin waɗannan zakoki masu zafin rai, ya Ubangiji!
7 Bari su ɓace kamar ruwan da ya tsanye,
Bari a murtsuke su kamar ciyayi a hanya.
8 Bari su zama kamar katantanwu waɗanda sukan narke su yi yauƙi,
Allah ya sa su zama kamar jinjirin da aka haifa matacce.
Wanda bai taɓa ganin hasken rana ba.
9 Kafin tukunya ta ji zafin wuta,
Da zafin fushi, Allah zai watsar da su tun suna da rai.
10 Adalai za su yi murna sa’ad da suka ga an hukunta masu zunubi,
Za su wanke ƙafafunsu cikin jinin mugaye.
11 Mutane za su ce, “Hakika an sāka wa adalai,
Hakika akwai Allah wanda yake shara’anta duniya!”