Addu’ar Neman Ceto daga Maƙiya
1 Ka cece ni daga maƙiyana, ya Allahna,
Ka kiyaye ni daga waɗanda suka tasar mini!
2 Ka cece ni daga waɗannan mugaye,
Ka tsirar da ni daga masu kisankan nan!
3 Duba! Suna jira su auka mini,
Mugaye suna taruwa gāba da ni,
Ba domin wani zunubi ko wani laifin da na yi ba,
4 Ba domin na yi wani laifi ba, ya Ubangiji,
Har da suka gaggauta gāba da ni.
Kai da kanka ka gani, ya Allah na Isra’ila!
Ka tashi ka taimake ni.
5 Ka tashi, ya Ubangiji, Allah Maɗaukaki, ka taimake ni,
Ka tashi ka hukunta al’ummai,
Kada ka yi wa waɗannan mugaye, maciya amana, jinƙai!
6 Da maraice suka komo,
Suna yaƙe haƙora kamar karnukan da suke yawo ko’ina a birni.
7 Ji abin da suke fada!
Harsunansu suna kama da takuba a bakinsu,
Duk da haka suna ta tambaya, suna cewa, “Wa zai ji mu?”
8 Amma kai dariya kake yi musu, ya Ubangiji,
Ka mai da al’ummai duka abin bandariya!
9 Mai tsarona, kai ne kake kiyaye ni,
Kai ne mafakata, ya Allah.
10 Allahna wanda yake ƙaunata, zai zo gare ni,
Zai sa in ga an kori magabtana.
11 Kada ka kashe su, ya Allah, don kada jama’ata su manta.
Ka watsar da su da ikonka, ka hallaka su ya Ubangiji mai kiyaye mu!
12 Zunubi na cikin leɓunansu, maganganunsu na zunubi ne,
Da ma a kama su saboda girmankansu,
Domin suna la’antarwa, suna ƙarya!
13 Da fushinka ka hallaka su,
Ka hallaka su ɗungum.
Sa’an nan jama’a za su sani Allah yana mulkin Isra’ila,
Mulkinsa ya kai ko’ina a duniya!
14 Da maraice maƙiyana suka komo,
Suna yaƙe haƙora kamar karnukan da suke yawo ko’ina a birni.
15 Suna kai da kawowa ko’ina neman abinci,
In ba su sami abin da ya ishe su ba,
Sukan yi gunaguni.
16 Amma zan raira waƙa a kan ikonka,
Kowace safiya zan raira waƙa da ƙarfi
Ga zancen madawwamiyar ƙaunarka.
Kai mafaka ne a gare ni,
Wurin ɓuya a kwanakin wahala.
17 Zan yabe ka, mai tsarona,
Allah ne mafakata,
Allah wanda ya ƙaunace ni.