Sa Zuciya ga Allah
1 Ya Allah, kai ne Allahna,
Ina sa zuciya gare ka.
Duk niyyata ta nemanka ce,
Raina yana ƙishinka,
Kamar bussasshiyar ƙasa,
Wadda ta zozaye, ba ta da ruwa.
2 Bari in gan ka a tsattsarkan wurinka,
In dubi ɗaukakarka da darajarka.
3 Madawwamiyar ƙaunarka ta fi rai kansa,
Saboda wannan zan yabe ka.
4 Muddin raina, zan yi maka godiya,
Zan ta da hannuwana sama, in yi addu’a gare ka.
5 Raina zai yi liyafa, yă ƙoshi sosai,
Ni kuwa zan raira waƙoƙin murna na yabo a gare ka.
6 Sa’ad da nake kwance a gadona na tuna da kai,
Dare farai ina ta tunawa da kai,
7 Domin kai kake taimakona kullayaumin.
Da murna, nake raira waƙa,
A inuwar fikafikanka,
8 Raina yana manne maka,
Ikonka yana riƙe da ni.
9 Waɗanda suke ƙoƙari su kashe ni,
Za su gangara zuwa lahira,
10 Za a kashe su cikin yaƙi,
Kyarketai kuwa za su cinye gawawwakinsu.
11 Sarki zai yi farin ciki ga Allah,
Duk waɗanda suka yi alkawarai da sunan Allah
Za su yi murna,
Amma za a rufe bakunan maƙaryata.