Kukan Neman Taimako
1 Ka cece ni, ya Allah!
Ruwa ya sha kaina.
2 Ina nutsewa cikin laka mai zurfi,
Ba kuwa ƙasa mai ƙarfi,
Na tsunduma cikin ruwa mai zurfi,
Raƙuman ruwa kuwa sun kusa kashe ni.
3 Na gaji da kira, ina neman taimako,
Maƙogwarona yana yi mini ciwo,
Idanuna duka sun gaji,
Saboda ina zuba ido ga taimakonka.
4 Waɗanda suke ƙina ba dalili
Sun fi gashin kaina yawa,
Waɗanda suke baza ƙarya suke ƙina,
Suna da ƙarfi, suna kuwa so su kashe ni.
Suka tilasta ni in mayar da abubuwan da ba satarsu na yi ba.
5 Zunubaina ba a ɓoye suke a gare ka ba ya Allah,
Ka san irin wawancin da na yi!
6 Kada ka bar ni in jawo kunya ga waɗanda suka dogara gare ka,
Ya Ubangiji Allah Mai Iko Dukka!
Kada ka bar ni in jawo abin kunya
Ga waɗanda suke maka sujada, ya Allah na Isra’ila!
7 Sabili da kai ne aka ci mutuncina,
Kunya ta rufe ni.
8 Kamar baƙo nake ga ‘yan’uwana,
Haka ma ga iyalina, kamar baƙo nake.
9 Ƙaunar da nake da ita ta yin ibada a Haikalinka
Tana iza ni a ciki kamar wuta,
Zargin da suke yi a kanka, ya fāɗa a kaina.
10 Na ƙasƙantar da kaina ta wurin yin azumi,
Jama’a kuwa suka ci mutuncina.
11 Na sa tufafin makoki,
Sai suka maishe ni abin dariya.
12 A tituna suna ta magana a kaina,
Bugaggu da giya kuwa suna raira waƙa a kaina.
13 Amma ni, zan yi addu’a gare ka, ya Ubangiji,
Ka amsa mini, ya Allah, a lokacin da ka zaɓa,
Sabili da muhimmiyar ƙaunarka,
Saboda kana cika alkawarinka na yin ceto.
14 Ka cece ni daga nutsewa cikin wannan laka,
Ka kiyaye ni daga maƙiyana,
Daga kuma wannan ruwa mai zurfi.
15 Kada ka bar ambaliyar ruwa ta rufe ni.
Kada ka bar ni in mutu cikin zurfafa,
Ko in nutse a cikin kabari.
16 Sabili da madawwamiyar ƙaunarka, ka amsa mini, ya Ubangiji,
Ka juyo wurina, saboda juyayinka mai girma!
17 Kada ka ɓoye kanka daga bawanka,
Ina shan babbar wahala, ka yi hanzari ka amsa mini!
18 Ka zo ka fanshe ni,
Ka kuɓutar da ni daga abokan gābana.
19 Ka san yadda ake cin mutuncina,
Da yadda ake kunyata ni, ake ƙasƙantar da ni,
Kana ganin dukan abokan gābana.
20 Zuciyata ta karai saboda cin mutuncin da ake ci mini,
Ni kuwa ba ni da mataimaki,
Na sa zuciya za a kula da ni,
Amma babu.
Na sa zuciya zan sami ta’aziyya,
Amma ban samu ba.
21 Sa’ad da na ji yunwa, sai suka ba ni dafi,
Sa’ad da na ji ƙishi, sai suka ba ni ruwan tsami.
22 Allah ya sa bukukuwansu su zama lalacewarsu,
Shagulgulansu kuma su zama sanadin fāɗuwarsu!
23 Ka makantar da su, har da ba za su iya gani ba,
Kullum ka sa bayansu ya ƙage!
24 Ka kwarara musu fushinka,
Bari zafin fushinka ya ci musu!
25 Allah ya sa su gudu su bar sansaninsu,
Kada wani ya ragu da rai cikin alfarwansu!
26 Sun tsananta wa waɗanda ka hukunta,
Suna taɗin shan wuyar waɗanda ka aukar wa cutar.
27 Ka riɓaɓɓanya zunubansu,
Kada ka bar su su sami rabon kome daga cikin cetonka.
28 Ka sa a goge sunansu daga cikin littafin rai,
Kada a sa su a lissafin jama’arka.
29 Amma ni mai bukata ne, ina shan wahala,
Ka tsame ni, ya Allah, ka cece ni!
30 Zan raira waƙar yabo ga Allah,
Zan yi shelar girmansa ta wurin yi masa godiya,
31 Wannan zai daɗaɗa wa Ubangiji rai
Fiye da hadayar bijimi,
Fiye da a ba shi bijimi bana bakwai.
32 Sa’ad da masu bukata suka ga wannan za su yi murna,
Waɗanda suke yi wa Allah sujada kuwa za a ƙarfafa su.
33 Ubangiji yana kasa kunne ga masu bukata,
Bai manta da jama’arsa da suke a kurkuku ba.
34 Ku yabi Allah, ku al’arshi da duniya, ku yabi Allah,
Tekuna da dukan talikan da suke cikinsu!
35 Gama zai ceci Sihiyona,
Ya sāke gina garuruwan Yahuza,
Jama’arsa za su zauna a wurin, su mallaki ƙasar.
36 Zuriyar bayinsa za su gāje ta,
Masu ƙaunarsa za su zauna a wurin.