Addu’ar Tsoho
1 A gare ka, ya Ubangiji, lafiya lau nake,
Faufau kada ka bari a yi nasara da ni!
2 Sabili da kai adali ne ka taimake ni, ka cece ni.
Ka kasa kunne gare ni, ka cece ni!
3 Ka zama mini lafiyayyiyar mafaka,
Da kagara mai ƙarfi, domin ka tsare ni,
Kai ne mafakata da kāriyata.
4 Ya Allahna, ka cece ni daga mugaye,
Daga ikon mugga, wato mugayen mutane.
5 Ya Ubangiji, a gare ka nake sa zuciya,
Tun ina yaro, nake dogara gare ka.
6 A duk kwanakina a gare ka nake dogara,
Kana kiyaye ni tun da aka haife ni,
Kullayaumi zan yabe ka!
7 Raina abin damuwa ne ga mutane da yawa,
Amma kai ne kāriyata mai ƙarfi.
8 Ina yabonka dukan yini,
Ina shelar darajarka.
9 Yanzu da na tsufa, kada ka yashe ni,
Yanzu da ƙarfina ya ƙare kuma, kada ka rabu da ni!
10 Maƙiyana, waɗanda suke so su kashe ni,
Suna magana, suna ƙulle-ƙulle gāba da ni.
11 Suna cewa, “Ai, Allah ya rabu da shi,
Gama ba wanda zai cece shi!”
12 Kada ka yi nisa da ni haka, ya Allah,
Ka yi hanzari ka taimake ni, ya Allahna!
13 Ka sa a kori waɗanda suka tasar mini,
A hallaka su!
Ka sa a kunyata waɗanda suke ƙoƙari su cuce ni,
A wulakanta su sarai!
14 A koyaushe zan sa zuciya gare ka,
Zan yi ta yabonka.
15 Zan ba da labarin adalcinka,
Zan yi magana a kan cetonka duk yini,
Ko da yake ya fi ƙarfin in san shi duka.
16 Zan tafi in yi yabon ikonka, ya Ubangiji Allah,
Zan yi shelar adalcinka,
Naka, kai kaɗai.
17 Kai ne ka koya mini, ya Allah, tun lokacin da nake yaro,
Har wa yau kuwa ina ba da labarin ayyukanka masu banmamaki.
18 Yanzu da na tsufa, na kuma yi furfura,
Kada ka rabu da ni, ya Allah!
Ka kasance tare da ni sa’ad da nake shelar ikonka da ƙarfinka ga mutanen dukan zamanai masu zuwa.
19 Adalcinka, ya Allah, ya kai har sammai.
Ka aikata manyan ayyuka,
Ba waninka!
20 Ka aiko mini da wahala da azaba,
Amma za ka mayar mini da ƙarfina,
Za ka tashe ni daga kabari.
21 Za ka girmama ni har abada,
Za ka sāke ta’azantar da ni.
22 Hakika zan yabe ka da garaya,
Zan yabi amincinka, ya Allahna.
Da garayata zan yi maka waƙoƙi,
Ya Mai Tsarki na Isra’ila.
23 Zan ta da muryar farin ciki
Sa’ad da nake raira maka waƙar yabbai,
Zan raira waƙa da zuciya ɗaya,
Gama dā ka fanshe ni.
24 Zan yi magana a kan adalcinka dukan yini,
Saboda an yi nasara da waɗanda suke ƙoƙari su cuce ni, sun ruɗe.