Mulkin Sarki Mai Adalci
1 Ka koya wa sarki ya yi shari’a
Da adalcinka, ya Allah,
Ka kuma ba shi shari’arka,
2 Don ya yi mulkin jama’arka bisa kan shari’a,
Ya kuma bi da mulki da adalci.
3 Ka sa ƙasar ta mori wadatarta,
Ka sa al’ummar ta san adalci.
4 Ka sa sarki ya yi wa talakawa shari’ar gaskiya,
Ya taimaki waɗanda suke da bukata,
Ya kuma hukunta azzalumai!
5 Ka sa su girmama ka
Muddin rana tana haskakawa,
Muddin wata yana ba da haske dukan lokaci.
6 Ka sa sarki ya zama kamar ruwan sama a gonaki,
Ya zama kamar yayyafi a bisa ƙasa.
7 Ka sa adalci ya bunƙasa a zamaninsa,
Wadata ta dawwama muddin wata na haskakawa.
8 Mulkinsa ya kai daga teku zuwa teku,
Daga Kogin Yufiretis, har zuwa iyakar duniya.
9 Kabilan hamada za su durƙusa a gabansa,
Abokan gābansa za su kwanta warwar a cikin ƙura.
10 Sarakunan Esbanya da na tsibirai,
Za su ba shi kyautai,
Sarakunan Arabiya da na Habasha
Za su kawo masa kyautai.
11 Dukan sarakuna za su durƙusa a gabansa,
Dukan sauran al’umma za su bauta masa!
12 Yakan ceci matalauta waɗanda suka yi kira gare shi,
Da waɗanda suke da bukata,
Da waɗanda ba a kula da su.
13 Yakan ji tausayin gajiyayyu da matalauta,
Yakan ceci rayukan waɗanda suke da bukata.
14 Yakan cece su daga zalunci da kama-karya,
Rayukansu suna da daraja a gare shi.
15 Ran sarki yă daɗe!
Da ma a ba shi zinariya daga Arabiya,
Da ma a yi masa addu’a dukan lokaci,
Allah ya sa masa albarka kullum!
16 Da ma a sami hatsi mai yawa a ƙasar,
Da ma amfanin gona yă cika tuddan,
Yă yi yawa kamar itatuwan al’ul na Lebanon,
Da ma birane su cika da mutane,
Kamar ciyayin da suke girma a sauruka.
17 Da ma a yi ta tunawa da sunansa har abada,
Da ma shahararsa ta ɗore muddin rana tana haskakawa.
Da ma dukan sauran al’umma su yabi sarkin,
Dukan jama’a su roƙi Allah yă sa musu albarka,
Kamar yadda ya sa wa sarki albarka.
18 Ku yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila,
Wanda shi kaɗai ne yake aikata al’amuran nan masu banmamaki!
19 Ku yabi sunansa mai daraja har abada,
Allah ya sa ɗaukakarsa ta cika dukan duniya!
Amin! Amin!
20 Ƙarshen addu’o’in Dawuda, ɗan Yesse ke nan.