Allah Ya Ƙasƙantar da Mugaye, Ya Ɗaukaka Adalai
1 Muna yabonka, ya Allah, muna yabonka!
Muna shelar sunanka mai girma,
Muna kuwa faɗa abubuwan banmamaki da ka aikata!
2 “Na ƙayyade lokacin yin shari’a,” in ji Ubangiji Allah,
“Zan kuwa yi shari’ar gaskiya.
3 Ko da duniya da dukan waɗanda yake zaune cikinta za su ɓace,
Zan ƙarfafa harsashin gininta.
4 Na faɗa wa masu girmankai kada su yi taƙama,
Na kuma faɗa wa mugaye kada su yi fāriya,
5 Na dai faɗa musu su daina yanga,
Su daina yin taƙama.”
6 Hukunci ba daga gabas, ko yamma,
Ko daga kudu, ko arewa yake zuwa ba.
7 Allah yake yin shari’a,
Yana ƙasƙantar da waɗansu, ya kuma ɗaukaka waɗansu.
8 Ubangiji yana riƙe da ƙoƙo,
Cike da sabon ruwan inabi mai ƙarfi,
Yana zuba shi, dukan mugaye kuwa suna ta sha,
Suka shanye shi ƙaƙaf.
9 Amma har abada ba zan daina yin magana a kan Allah na Yakubu ba,
Ko in daina raira yabbai gare shi.
10 Shi zai karya ikon mugaye,
Amma za a ƙara wa masu adalci ƙarfi.