Alkawarin Allah da Dawuda
1 Ya Ubangiji zan raira waƙar
Madawwamiyar ƙaunarka koyaushe,
Zan yi shelar amincinka a dukan lokaci.
2 Na sani ƙaunarka za ta dawwama har abada,
Amincinka kuma tabbatacce ne kamar sararin sama.
3 Ka ce, “Na yi alkawari da mutumin da na zaɓa,
Na yi wa bawana Dawuda alkawari cewa,
4 ‘Daga zuriyarka kullum za a sami sarki,
Zan kiyaye mulkinka har abada.’ ”
5 Talikan da suke Sama suna raira waƙa a kan
Abubuwan banmamakin da kake yi,
Suna raira waƙa kan amincinka, ya Ubangiji.
6 Ba wani kamarka a Sama, ya Ubangiji,
Ba wani daga su cikin talikai da yake daidai da kai.
7 Ana girmama ka a cikin majalisar talikai,
Duk waɗanda suke kewaye da kai suna yin tsoronka ƙwarai.
8 Ya Ubangiji Allah, Mai Runduna,
Ba wani mai iko kamarka,
Kai mai aminci ne a kowane abu.
9 Kai kake mulkin haukan teku,
Kakan kwantar da haukan raƙuman ruwa.
10 Ka ragargaza dodon nan Rahab, ka kashe shi,
Da ƙarfin ikonka ka cinye maƙiyanka.
11 Duniya taka ce, haka ma samaniya taka ce,
Kai ne ka halicci duniya da dukan abin da yake cikinta.
12 Kai ne ka yi kudu da arewa,
Dutsen Tabor da Dutsen Harmon
Suna raira waƙa gare ka don farin ciki.
13 Kai kake da iko!
Kai kake da ƙarfi!
14 A gaskiya da adalci aka kafa mulkinka,
Akwai ƙauna da aminci a dukan abin da kake yi.
15 Masu farin ciki ne jama’ar da suke yi maka sujada, suna raira waƙoƙi,
Waɗanda suke zaune a hasken alherinka.
16 Suna murna dukan yini saboda da kai,
Suna kuwa yabonka saboda alherinka.
17 Kana sa mu ci babbar nasara,
Da alherinka kakan sa mu yi rinjaye,
18 Sabili da ka zaɓar mana mai kāre mu,
Kai, Mai Tsarki na Isra’ila,
Kai ne ka ba mu sarkinmu.
19 Ka faɗa wa amintattun bayinka a wahayin da ka nuna musu tun da daɗewa, ka ce,
“Na sa kambin sarauta a kan shahararren soja,
Na ba da gadon sarauta ga wanda aka zaɓa daga cikin jama’a.
20 Na zaɓi bawana Dawuda,
Na naɗa shi sarkinku.
21 Ƙarfina zai kasance tare da shi,
Ikona kuma zai ƙarfafa shi.
22 Abokan gābansa ba za su taɓa cin nasara a kansa ba,
Mugaye ba za su kore shi ba.
23 Zan ragargaza magabtansa,
In karkashe duk waɗanda suke ƙinsa.
24 Zan ƙaunace shi kullum, in amince da shi,
Zan sa ya yi nasara kullayaumin.
25 Zan faɗaɗa mulkinsa tun daga Bahar Rum,
Har zuwa Kogin Yufiretis.
26 Zai ce mini, ‘Kai ubana ne da Allahna,
Kai ne kake kiyaye ni, kai ne Mai Cetona.’
27 Zan maishe shi ɗan farina,
Mafi girma daga cikin dukan sarakuna.
28 Zan riƙa ƙaunarsa har abada,
Alkawarin da na yi da shi kuma zai tabbata har abada.
29 A kullayaumin daga cikin zuriyarsa ne za a naɗa sarki,
Mulkinsa zai dawwama kamar sararin sama.
30 “Amma idan zuriyarsa sun ƙi yin biyayya da shari’ata,
Ba su kuwa zauna cikin ka’idodina ba,
31 In sun ƙyale koyarwata,
Ba su kiyaye umarnaina ba,
32 To, sai in hukunta su saboda zunubansu,
Zan bulale su saboda laifofinsu.
33 Amma fa, ba zan daina ƙaunar Dawuda ba,
Ba kuwa zan rasa cika alkawarin da na yi masa ba.
34 Ba zan keta alkawarin da na yi masa ba,
Ba zan soke ko ɗaya daga cikin alkawaran da na yi masa ba.
35 “Da sunana mai tsarki na yi alkawari sau ɗaya tak,
Ba zan yi wa Dawuda ƙarya ba!
36 Zuriyarsa za ta kasance kullum,
Zan lura da mulkinsa muddin rana tana haskakawa.
37 Zai dawwama kamar wata,
Kamar amintaccen mashaidin nan da yake a sararin sama.”
38 Amma kana fushi da zaɓaɓɓen sarkinka,
Ka rabu da shi, ka yashe shi.
39 Ka soke alkawarinka wanda ka yi wa bawanka,
Ka jefar da kambinsa a cikin ƙazanta.
40 Ka rurrushe garun birninsa,
Ka mai da sansaninsa mai kagara kufai.
41 Dukan waɗanda suke wucewa za su sace masa kayansa,
Maƙwabtansa duka suna yi masa ba’a.
42 Ka ba maƙiyansa nasara,
Ka sa dukansu su yi murna.
43 Ka sa makamansa su zama marasa amfani,
Ka bari a ci shi da yaƙi.
44 Ka ƙwace masa sandan sarautarsa,
Ka buge gadon sarautarsa ƙasa.
45 Ka sa shi ya tsofe kafin lokacinsa,
Ka rufe shi da kunya.
46 Har yaushe za ka ɓoye kanka, ya Ubangiji?
Har abada ne?
Har yaushe fushinka zai yi ta ci kamar wuta?
47 Ka tuna kwanakin mutum kaɗan ne, ya Ubangiji,
Ka tuna yadda ka halicci mutane duka masu mutuwa ne!
48 Wa zai rayu har abada, ba zai mutu ba?
Ƙaƙa mutum zai hana kansa shiga kabari?
49 Ya Ubangiji, ina ƙaunarka ta dā?
Ina alkawaran nan waɗanda ka yi wa Dawuda?
50 Kada ka manta da yadda aka ci mutuncina, ni da nake bawanka,
Da yadda na daure da dukan cin mutuncin da arna suka yi mini.
51 Ya Ubangiji, kada ka manta da yadda maƙiyanka
suka ci mutuncin zaɓaɓɓen sarki da ka naɗa!
Suka yi ta cin mutuncinsa duk inda ya tafi.
52 Mu yabi Ubangiji har abada! Amin! Amin!