Waƙar Yabo
1 Abu mai kyau ne a yi wa Ubangiji godiya,
A raira waƙa don girmansa, Allah mafi ɗaukaka,
2 A yi shelar madawwamiyar ƙaunarka kowace safiya,
Amincinka kuma kowane maraice,
3 Da abubuwan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya,
Da amon garaya mai daɗi.
4 Ya Ubangiji,
Ayyukanka masu iko suna sa ni murna,
Saboda abin da ka aikata
Ina raira waƙa domin farin ciki.
5 Ayyukanka da girma suke, ya Ubangiji!
Tunaninka da zurfi suke!
6 Ga wani abin da wawa ba zai iya sani ba,
Dakiki kuma ba zai iya ganewa ba,
7 Shi ne mai yiwuwa ne mugu ya yi girma kamar tsire-tsire,
Masu aikata mugayen ayyuka kuma su arzuta,
Duk da haka za a hallaka su ɗungum.
8 Gama kai, ya Ubangiji,
Maɗaukaki ne har abada.
9 Mun sani maƙiyanka za su mutu,
Dukan mugaye kuwa za a yi nasara da su.
10 Ka sa ni na yi ƙarfi kamar bijimi mai faɗa,
Ka sa mini albarka da farin ciki.
11 Na ga fāɗuwar maƙiyana,
Na ji kukan mugaye.
12 Adalai za su yi yabanya
Kamar itatuwan giginya,
Za su yi girma kamar itatuwan al’ul na Lebanon.
13 Za su zama kamar itatuwan da aka daddasa a Haikalin Ubangiji,
Suna ta yabanya a Haikalin Allahnmu.
14 Waɗanda suke yin ‘ya’ya da tsufansu,
A kullum kuwa kore shar suke,
Suna da ƙarfinsu kuma.
15 Wannan ya nuna Ubangiji adali ne,
Shi wanda yake kāre ni,
Ba kuskure a gare shi.