Addu’ar Neman Sakayya
1 Ya Ubangiji, kai Allah ne wanda yake yin hukunci,
Ka bayyana fushinka!
2 Kai ne mai yi wa dukan mutane shari’a,
Ka tashi, ka sāka wa masu girmankai
Abin da ya dace da su!
3 Har yaushe mugaye za su yi ta murna?
Har yaushe ne, ya Ubangiji?
4 Har yaushe za su yi shakiyanci,
Su yi ta ɗaga kai?
Har yaushe, ya Ubangiji?
5 Suna ragargaza jama’arka, ya Ubangiji,
Suna zaluntar waɗanda suke naka.
6 Suna karkashe gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu,
Da kuma baƙin da suke zaune a ƙasarmu.
7 Suna cewa, “Ai, Ubangiji ba ya ganinmu,
Allah na Isra’ila ba ya lura da abin da yake faruwa!”
8 Ya jama’ata, ƙaƙa kuka zama dakikai, wawaye haka?
Sai yaushe za ku koya?
9 Allah ya yi mana kunnuwa, shi ba zai ji ba?
Allah ya yi mana idanu, shi ba zai gani ba?
10 Shi ne yake shugabancin sauran al’umma, ba zai hukunta su ba?
Shi ne yake koya wa dukan mutane, shi ba shi da sani ne?
11 Ubangiji ya san tunaninsu,
Ya san kuma hujjojinsu na rashin hankali.
12 Ya Ubangiji, mai farin ciki ne mutumin da kake koya wa,
Mutumin da kake koya masa shari’arka.
13 Don ka ba shi hutawa a kwanakin wahala,
Kafin a haƙa wa mugaye kabari.
14 Ubangiji ba zai rabu da jama’arsa ba,
Ba zai rabu da waɗanda suke nasa ba.
15 Adalci kuma zai sāke dawowa cikin majalisun alƙalai,
Dukan adalai kuwa za su yi na’am da shi.
16 Wa zai tsaya mini gāba da mugaye?
Wa zai goyi bayana gāba da masu aikata mugunta?
17 Da ba domin Ubangiji ya taimake ni ba,
Ai, da tuni na kai ƙasar da ba a motsi.
18 Na ce, “Ina kan fāɗuwa,”
Amma, ya Ubangiji, madawwamiyar ƙaunarka ta riƙe ni.
19 Sa’ad da nake alhini, ina cikin damuwa,
Ka ta’azantar da ni, ka sa in yi murna.
20 Ba ruwanka da alƙalai azzalumai, marasa gaskiya,
Waɗanda suka mai da rashin gaskiya ita ce gaskiyarsu,
21 Sukan shirya wa mutanen kirki maƙarƙashiya,
Sukan yanke wa marar laifi hukuncin kisa.
22 Amma Ubangiji yakan kāre ni,
Allahna yakan kiyaye ni.
23 Shi zai hukunta su saboda muguntarsu,
Ya hallaka su saboda zunubansu.
Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.