Waƙar Yabo da Sujada
1 Ku zo mu yabi Ubangiji!
Mu raira waƙa domin farin ciki ga mai kiyaye mu,
Da Mai Cetonmu!
2 Mu zo gabansa da godiya,
Mu raira waƙoƙin farin ciki na yabo!
3 Gama Ubangiji Allah ne mai iko,
Shi yake mulki bisa sauran alloli duka.
4 Yana mulki bisa dukan duniya,
Daga zurfafan kogwannin duwatsu zuwa tuddai mafiya tsayi.
5 Yana mulki bisa tekun da ya yi,
Da kuma bisa ƙasar da ya siffata.
6 Ku zo, mu durƙusa, mu yi masa sujada,
Mu durƙusa a gaban Ubangiji, Mahaliccinmu!
7 Shi ne Allahnmu,
Mu ne jama’ar da yake lura da ita,
Mu ne kuma garken da yake ciyarwa.
Yau ku ji abin da yake faɗa.
8 “Kada ku taurare zuciyarku yadda kakanninku suka yi a Meriba,
Kamar yadda suka yi a jeji a Masaha, a wancan rana.
9 A can suka gwada ni suka jarraba ni,
Ko da yake da idanunsu suka ga abin da na yi dominsu.
10 A shekara arba’in ɗin nan,
Jama’ar nan ta zama abar ƙyama gare ni,
‘Su marasa biyayya ne,’ in ji ni,
‘Gama sun ƙi bin umarnaina!’
11 Sai na ji haushi, na yi musu alkawari mai nauyi.
Na ce, ‘Faufau ba za ku shiga ƙasar da zan ba ku hutawa a ciki ba.’ ”