ZAF 1

Ranar Hasalar Ubangiji a kan Yahuza

1 Ubangiji ya yi magana da Zafaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon, Sarkin Yahuza.

2 “Ni Ubangiji na ce, zan shafe dukan kome

Da yake a duniya.

3 Zan shafe mutum da dabba,

Zan shafe tsuntsayen sararin sama da kifayen teku,

Zan kuma rushe gumakansu tare da mugaye,

Zan kuma datse ɗan adam daga duniya.

4 “Zan miƙa hannuna gāba da Yahuza

Da dukan mazaunan Urushalima.

A wurin nan zan datse saura waɗanda suke bauta wa Ba’al,

Da kuma sunayen firistocin gumaka tare da firistocina,

5 Da kuma waɗanda suke durƙusa wa rundunan sama a kan bene,

Waɗanda sukan durƙusa, su rantse da Ubangiji,

Duk da haka kuma sai su rantse da Milkom,

6 Da kuma waɗanda suka juya, suka bar bin Ubangiji,

Waɗanda ba su neman Ubangiji, ba su kuma roƙonsa.”

7 Ku yi tsit a gaban Ubangiji Allah!

Gama ranar Ubangiji ta gabato.

Ubangiji ya shirya ranar shari’a,

Ya kuma keɓe waɗanda za su aikata hukuncinsa.

8 “A ranar shari’a, ni Ubangiji zan hukunta shugabanni da hakimai,

Da dukan waɗanda suke bin al’adun ƙasashen waje.

9 A wannan rana zan hukunta duk wanda yake tsalle a bakin ƙofa,

Da waɗanda suke cika gidan maigidansu da zalunci da ha’inci.

10 “Ni Ubangiji na ce, a wannan rana, za a ji kuka a Ƙofar Kifi,

Za a ji kururuwa kuma daga unguwa ta biyu,

Da amon ragargajewa daga kan tuddai.

11 Ku yi kururuwa, ku mazaunan Maktesh,

Gama ‘yan kasuwa sun ƙare,

An kuma datse dukan waɗanda suke awon azurfa.

12 “A lokacin nan,

Zan bincike Urushalima da fitilu,

Zan kuwa hukunta marasa kulawa

Waɗanda suke zaman annashuwa,

Waɗanda suke cewa a zukatansu,

‘Ubangiji ba zai yi alheri ba,

Ba kuma zai yi mugunta ba!’

13 Za a washe dukiyarsu,

Za a kuwa rurrushe gidajensu,

Ko da yake sun gina gidaje, ba za su zauna a ciki ba,

Ko da yake sun dasa inabi, ba za su sha ruwansa ba.”

14 Babbar ranar Ubangiji ta gabato,

Tana gabatowa da sauri.

Ku ji muryar ranar Ubangiji!

Jarumi zai yi kuka mai zafi.

15 Wannan rana ta hasala ce,

Ranar azaba da wahala,

Ranar lalatarwa da hallakarwa,

Ranar duhu baƙi ƙirin,

Ranar gizagizai da baƙin duhu,

16 Ranar busar ƙaho da yin kururuwar yaƙi

Gāba da birane masu garu da hasumiyai masu tsawo.

17 “Zan aukar wa mutane da wahala,

Za su kuwa yi tafiya kamar makafi,

Domin sun yi wa Ubangiji zunubi.

Za a zubar da jininsu kamar ƙura,

Namansu kuwa kamar taroso.”

18 Azurfarsu da zinariyarsu ba za su cece su

A ranar hasalar Ubangiji ba,

A cikin zafin kishinsa

Dukan duniya za ta hallaka.

Zai kawo ƙarshen duniya duka nan da nan.