Alkawarin Mai Ceto
1 Ku roƙi ruwan sama daga wurin Ubangiji a lokacin bazara,
Gama Ubangiji ne yake yin gizagizan hadiri,
Shi ne yake bai wa mutane yayyafi.
Shi ne kuma yake ba kowane mutum tsire-tsiren saura.
2 Gama maganar shirme kan gida yake yi,
Masu dūba suna ganin wahayin ƙarya,
Masu mafarkai suna faɗar ƙarya,
Ta’aziyyarsu ta banza ce.
Domin haka mutane suna ta yawo kamar tumaki,
Suna shan wahala saboda rashin makiyayi.
3 Ubangiji ya ce,
“Ina fushi ƙwarai da makiyayan,
Zan kuwa hukunta shugabannin,
Gama ni Ubangiji Mai Runduna zan lura da garkena,
Wato jama’ar Yahuza.
Zan mai da su dawakaina na yaƙi.
4 Daga cikinsu za a sami mafificin dutsen gini,
Daga cikinsu kuma za a sami turken alfarwa,
Daga cikinsu za a sami bakan yaƙi,
Daga cikinsu kuma kowane mai mulki zai fito.
5 Za su zama kamar ƙarfafan mutane cikin yaƙi,
Za su tattaka maƙiyi a cikin taɓon tituna.
Za su yi yaƙi, gama Ubangiji yana tare da su,
Za su kunyatar da sojojin doki.
6 “Zan sa jama’ar Yahuza ta yi ƙarfi,
Zan ceci jama’ar Yusufu.
Zan dawo da su domin ina jin tausayinsu.
Za su zama kamar waɗanda ban taɓa ƙyale su ba,
Gama ni Ubangiji Allahnsu ne,
Zan amsa musu.
7 Sa’an nan mutanen Ifraimu za su zama kamar ƙarfafan jarumawa,
Za su yi farin ciki kamar sun sha ruwan inabi,
‘Ya’yansu za su gani su yi murna,
Zukatansu za su yi murna da Ubangiji.
8 “Zan yafato su in tattaro su,
Gama zan fanshe su,
Zan sa su su yi yawa kamar yadda suke yi a dā.
9 Ko da yake na watsar da su cikin al’ummai,
Duk da haka za su riƙa tunawa da ni daga ƙasashe masu nisa.
Su da ‘ya’yansu za su rayu, su komo.
10 Zan dawo da su gida daga ƙasar Masar,
In tattaro su daga Assuriya,
Zan kawo su a ƙasar Gileyad da ta Lebanon,
Har su cika, ba sauran wuri.
11 Za su bi ta cikin tekun wahala,
Zan kwantar da raƙuman teku,
Kogin Nilu zai ƙafe duk da zurfinsa,
Za a ƙasƙantar da Assuriya,
Sandan sarautar Masar zai rabu da ita.
12 Zan ƙarfafa su,
Za su yi tafiya da sunansa,
Ni Ubangiji na faɗa.”