Urushalima da Sauran Al’umma
1 Ga ranar Ubangiji tana zuwa sa’ad da za a raba ganimar da aka ƙwace daga gare ku a kan idonku.
2 Gama zan tattara dukan al’ummai su yi yaƙi da Urushalima. Za a ci birnin, a washe gidajen. Za a yi wa mata faɗe. Za a kai rabin mutanen birnin bauta, amma za a bar sauran mutanen a cikin birnin.
3 Sa’an nan Ubangiji zai tafi ya yi yaƙi da waɗannan al’ummai kamar yadda ya yi a dā.
4 A wannan rana ƙafafunsa za su tsaya a bisa Dutsen Zaitun wanda yake wajen gabas da Urushalima. Dutsen Zaitun zai tsage biyu daga gabas zuwa yamma, ya zama babban kwari. Sashi guda na dutsen zai janye zuwa wajen kudu. Ɗaya sashin kuma zai janye zuwa wajen arewa.
5 Za ku gudu zuwa kwarin duwatsuna, gama kwarin duwatsu zai kai har Azel, kamar yadda kakanninku suka gudu a zamanin Azariya, Sarkin Yahuza, a lokacin da aka yi girgizar ƙasa. Sa’an nan Ubangiji Allahna zai zo tare da dukan tsarkakansa!
6 A wannan rana ba haske. Masu ba da haske za su dushe.
7 Ubangiji ne ya san wannan rana. Ba rana ba dare. Da maraice ma akwai haske.
8 A wannan rana ruwa mai rai zai gudano daga Urushalima. Rabinsa zai nufi tekun Gishiri, rabi kuma zai nufi Bahar Rum. Zai riƙa malalowa rani da damuna.
9 A ranar, Ubangiji zai zama Sarkin Duniya duka, zai kuma zama shi ne Ubangiji shi kaɗai, ba wani suna kuma sai nasa.
10 Ƙasa dukka za ta zama fili, daga Geba zuwa Rimmon a kudancin Urushalima. Amma Urushalima za ta kasance a kan tudu, za ta miƙe daga Ƙofar Biliyaminu, zuwa wurin da ƙofa ta fari take a dā, har zuwa Ƙofar Kusurwa, sa’an nan ta miƙe daga Hasumiyar Hananel zuwa wuraren matsewar ruwan inabin sarki.
11 Za a zauna cikin Urushalima lami lafiya, ba sauran la’ana.
12 Ga annobar da Ubangiji zai bugi dukan al’ummai da ita, wato su da suka tafi su yi yaƙi da Urushalima. Naman jikunansu zai ruɓe lokacin da suke a tsaye. Idanunsu kuma za su ruɓe cikin kwarminsu. Harsunansu za su ruɓe a bakunansu.
13 A wannan rana babbar gigicewa daga wurin Ubangiji za ta faɗo musu, har kowa zai kama hannun ɗan’uwansa, ya kai masa dūka.
14 Mutanen Yahuza za su yi yaƙi don su kāre Urushalima. Za a kuma tattara dukan dukiyar al’umman da suke kewaye, su zinariya, da azurfa, da riguna tuli.
15 Annoba irin wannan kuma za ta faɗo wa dawakai da alfadarai, da raƙuma, da jakuna, da dukan dabbobin da suke cikin sansaninsu.
16 Sa’an nan wanda ya ragu daga cikin dukan al’umman da suka kai wa Urushalima yaƙi zai riƙa haurawa zuwa Urushalima kowace shekara, domin yi wa Ubangiji Maɗaukakin Sarkin sujada a lokacin kiyaye Idin Bukkoki.
17 Idan kuwa wata al’umma a duniya ba ta haura zuwa Urushalima domin ta yi wa Ubangiji Maɗaukakin Sarki sujada ba, ba za a yi mata ruwan sama ba.
18 Idan al’ummar Masar ba ta halarci Idin Bukkoki ba, ba za a yi mata ruwan sama ba. Ubangiji kuma zai kawo mata irin annobar da ya kawo wa al’umman da suka ƙi halartar Idin Bukkoki.
19 Wannan shi ne hukuncin da za a yi wa Masar da dukan al’umman da suka ƙi halartar Idin Bukkoki.
20 A wannan rana za a zāna waɗannan kalmomi, wato “Mai Tsarki ga Ubangiji” a kan ƙararrawar dawakai. Tukwanen da suke Haikalin Ubangiji za su zama kamar kwanonin da suke a gaban bagade.
21 Kowace tukunya da take a Urushalima da Yahuza za ta zama tsattsarka ga Ubangiji Mai Runduna domin dukan masu miƙa hadaya su ɗauka su dafa naman hadaya a cikinsu. A wannan rana ba za a ƙara samun mai ciniki a Haikalin Ubangiji Mai Runduna ba.