Ubangiji zai Sāke Rayar da Urushalima
1 Ubangiji Mai Runduna kuma ya yi magana da ni, ya ce,
2 “Ni Ubangiji Mai Runduna ina kishin Sihiyona ƙwarai.
3 Zan koma wurin Sihiyona, in zauna a tsakiyar Urushalima. Za a ce da Urushalima birnin gaskiya, da kuma dutsen Ubangiji Mai Runduna, tsattsarkan dutse.
4 Tsofaffi, mata, da maza, za su zauna a titunan Urushalima, kowa yana tokare da sanda saboda tsufa.
5 Samari da ‘yan mata zan sa su cika titunan Urushalima, suna wasa.
6 “Idan abin nan ya zama mawuyaci ga sauran jama’a a kwanakin nan, zai zama mawuyacin abu ne a gare ni?
7 Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, zan ceci mutanena daga ƙasar gabas da ƙasar yamma.
8 Zan kawo su su zauna a Urushalima. Za su zama jama’ata, ni kuma zan zama Allahnsu da gaskiya da adalci.
9 “Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, ku himmantu, ku da kuke jin magana ta bakin annabawa a waɗannan kwanaki tun lokacin da aka ɗora harsashin ginin Haikalin Ubangiji Mai Runduna, don a gina Haikalin.
10 Gama kafin waɗannan kwanaki, mutum da dabba ba su da abin yi. Ba kuma zaman lafiya ga mai fita da shiga saboda maƙiya, gama na sa kowane mutum ya ƙi ɗan’uwansa.
11 Amma yanzu ba zan yi da sauran jama’an nan kamar yadda na yi a kwanakin dā ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
12 Gama za a yi shuka da salama. Kurangar inabi za ta yi ‘ya’ya, ƙasa kuma za ta ba da amfani, za a yi isasshen ruwan sama. Ni kuwa zan sa sauran jama’an nan su ci moriyar abubuwan nan duka.
13 Ya jama’ar Yahuza da jama’ar Isra’ila, kamar yadda kuka zama abin la’antarwa a cikin al’ummai, haka kuma zan cece ku, ku zama masu albarka, kada ku ji tsoro, amma ku himmantu.
14 “Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce, kamar yadda na ƙudura in aukar muku da masifa, ban kuwa fasa ba, lokacin da kakanninku suka tsokane ni, suka sa na yi fushi.
15 Haka kuma na ƙudura a waɗannan kwanaki in yi wa Urushalima da jama’ar Yahuza alheri. Kada ku ji tsoro!
16 Abubuwan da za ku yi ke nan, ku faɗa wa juna gaskiya, ku yi shari’a ta gaskiya a majalisunku, domin zaman lafiya.
17 Kada ku ƙulla wa junanku sharri, kada kuma ku so yin rantsuwa ta ƙarya, gama ina ƙin waɗannan abubuwa duka, ni Ubangiji na faɗa.”
18 Ubangiji Mai Runduna ya yi magana da ni, ya ce,
19 “Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, azumi na watan huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai, da na watan goma, za su zama lokatan murna, da farin ciki, da idodin farin ciki, ga jama’ar Yahuza, saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.
20 “Mutanen birane da yawa za su hallara.
21 Mutanen wani birni za su tafi wurin mutanen wani birni, su ce musu, ‘Za mu tafi mu roƙi alherin Ubangiji, mu kuma nemi Ubangiji Mai Runduna. Ku zo mu tafi.’
22 Jama’a da yawa da al’ummai masu iko za su zo Urushalima su nemi Ubangiji Mai Runduna, su kuma roƙi alherin Ubangiji.
23 Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, a waɗannan kwanaki mutum goma daga kowace al’umma da kowane harshe za su kama kafa wurin Bayahude, su ce, ‘Ka yardar mana mu tafi tare da kai, gama mun ji Allah yana tare da ku.’ ”