Sarauniyar Sheba Ta Ziyarci Sulemanu
1 Sarauniyar Sheba ta ji labarin sunan da Sulemanu ya yi ta dalilin sunan Ubangiji, ta zo don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya.
2 Ta iso Urushalima da ‘yan rakiya da yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya da yawa, da duwatsu masu daraja. Sa’ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa duk abin da yake a ranta.
3 Sulemanu ya amsa tambayoyinta dukka, ba abin da ya gagare shi amsawa.
4-5 Sarauniyar Sheba ta yi mamaki sa’ad da ta ga hikimar Sulemanu, da gidan da ya gina, da irin abincinsa, da irin zaman fādawansa, da yadda ma’aikatan gida suke hidima, da irin tufafinsu, da masu ba da abin sha, da hadayu na ƙonawa waɗanda yakan miƙa cikin Haikalin Ubangiji.
6 Sai ta ce wa Sulemanu, “Labarin da na ji a ƙasata a kan al’amuranka da hikimarka, gaskiya ne.
7 Amma ban gaskata da labarin ba, sai da na zo na gani da idona, ashe, ko rabi ma ba a faɗa mini ba, gama hikimarka da wadatarka sun fi abin da na ji.
8 Jama’arka, da fādawanka waɗanda suke tsaye a gabanka kullum, sun yi sa’a gama suna jin hikimarka.
9 Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka wanda ya yarda da kai, ya sa ka a kan gadon sarautar Isra’ila, domin Ubangiji yana ƙaunar Isra’ila har abada, ya naɗa ka sarki domin ka zartar da shari’a da adalci.”
10 Sa’an nan Sarauniyar Sheba ta ba sarki talanti ɗari da ashirin na zinariya,da kayan yaji mai yawan gaske, da duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa kamar yadda Sarauniyar Sheba ta kawo wa sarki Sulemanu ba.
11 Bayan wannan kuma jiragen ruwa na Hiram da suka kawo zinariya daga Ofir, sun kuma kawo itacen almug da yawa, da duwatsu masu daraja daga can.
12 Da itacen almug ne sarki ya yi ginshiƙai na Haikalin Ubangiji da gidan sarki, ya kuma yi molaye da garayu domin mawaƙa. Har wa yau ba a taɓa samu, ko ganin irin itacen almug kamar wannan ba.
13 Sarki Sulemanu ya ba Sarauniyar Sheba duk abin da ta nuna tana bukata, banda kyautar karamcin da ya yi mata. Sai ta koma ƙasarta tare da barorinta.
Dukiyar Sulemanu da Shahararsa
14 Yawan zinariya da akan kawo wa Sulemanu kowace shekara yakan kai talanti ɗari shida da sittin da shida na zinariya.
15 Banda wanda ya sa wa ‘yan kasuwa, da fatake, da harajin dukan sarakunan Arabiya, da na hakimai.
16 Sarki Sulemanu ya yi manyan garkuwoyi guda ɗari biyu da zinariya. Anyi kowace garkuwa da shekel ɗari shida na zinariya.
17 Ya kuma yi waɗansu garkuwoyi guda ɗari uku da zinariya. An yi kowace garkuwa da shekel dari uku na zinariya. Sarki kuwa ya ajiye su a ɗakin da aka gina da katakai daga Lebanon.
18 Ya kuma yi babban gadon sarauta na hauren giwa, sa’an nan ya dalaye shi da tattacciyar zinariya.
19 Gadon sarautar yana da matakai shida da siffar kan maraƙi a bayan gadon sarautar, a kowane gefen mazaunin kuma, akwai wurin ɗora hannu da siffofin zaki biyu suna tsaye a gefen wuraren ɗora hannun.
20 Akwai siffar zaki goma sha biyu suna tsaye a kowane gefen matakan nan shida. Ba a taɓa yin irinsu a kowace masarauta ba.
21 Dukan finjalai na sarki Sulemanu, da zinariya aka yi su, haka kuma finjalan da suke cikin ɗakin da aka gina da katakai daga Lebanon, ba a yi wani finjali da azurfa ba, domin ba a mai da azurfa kome ba a kwanakin Sulemanu.
22 Gama sarki yana da rundunar jiragen ruwa a tekun Tarshish tare da na Hiram. Sau ɗaya a shekara uku rundunar jiragen ruwa na Tarshish sukan kawo zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da birai, da ɗawusu masu daraja.
23 Sarki Sulemanu ya fi dukan sarakunan duniya dukiya da hikima.
24 Dukansu suna so su zo wurin Sulemanu don su ji hikimarsa wadda Allah ya ba shi.
25 Kowannensu yakan kawo masa yawan kyautai na kayayyakin azurfa, da na zinariya, da riguna, da turare, da kayan yaji, da dawakai, da alfadarai kowace shekara.
Kasuwancin Sulemanu a kan Dawakai da Karusai
26 Sulemanu kuwa ya tattara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), waɗanda ya zaunar da su a biranen karusai da kuma waɗansu tare da shi a Urushalima.
27 Sarki ya sa azurfa ta gama gari, kamar dai duwatsu a Urushalima, itacen al’ul kuma ya zama kamar jumaiza na Shefela.
28 Sulemanu kuwa ya sayo dawakai daga Masar da Kuye. ‘Yan kasuwar sarki sukan sayo dawakai daga Kuye a kan tamaninsu.
29 Akan sayo karusa a Masar a bakin azurfa ɗari shida, doki kuwa a bakin ɗari da hamsin, ‘yan kasuwar sarki sukan sayar da su ga dukan sarakunan Hittiyawa da na Suriyawa.