Iliya ya Koma gun Ahab
1 Bayan ‘yan kwanaki, sai Ubangiji ya yi magana da Iliya a shekara ta uku, ya ce, “Tafi, ka nuna kanka ga Ahab, ni kuwa zan sa a yi ruwan sama.”
2 Sai Iliya ya tafi.
A lokacin kuwa yunwa ta tsananta a Samariya.
3 Ahab kuwa ya kira Obadiya, shugaban gidansa. Obadiya kuwa mai tsoron Ubangiji ne sosai.
4 A lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji, Obadiya ya kwashe annabawa ɗari ya raba su hamsin hamsin ya ɓoye su a kogo, ya ciyar da su, ya shayar da su.
5 Sai Ahab ya ce wa Obadiya, “Ka tafi ko’ina a ƙasar duk inda maɓuɓɓugan ruwa suke, da inda fadamu suke duka, watakila ma sami ciyawa mu ceci rayukan dawakai da alfadarai, don kada mu rasa waɗansu.”
6 Saboda haka suka rabu biyu don su zagaya. Ahab ya bi waje guda, shi kuma ya bi ɗaya wajen.
7 Sa’ad da Obadiya yake tafiya a hanya suka yi kaciɓis da Iliya, Obadiya kuwa ya rabe da shi, sai ya rusuna ya ce, “Shugabana Iliya, kai ne kuwa?”
8 Iliya ya amsa masa ya ce, “Ni ne. Tafi, ka faɗa wa shugabanka, sarki, cewa ga ni nan.”
9 Obadiya ya ce, “Wane laifi na yi, har da za ka ba da ni a hannun Ahab ya kashe ni?
10 Na rantse da Ubangiji Allahnka mai rai, ba al’umma ko mulki da shugabana sarki bai aika a nemo ka ba. In suka ce ba ka nan, sai ya sa mulkin ko al’ummar su rantse, cewa ai, ba su same ka ba.
11 Yanzu kuwa ka ce, in tafi in faɗa masa, cewa ga ka a nan?
12 Rabuwata da kai ke da wuya, sai Ruhun Ubangiji ya kai ka wurin da ban sani ba, don haka, in na tafi na faɗa wa Ahab, in bai same ka ba, to, ni zai kashe, ko da yake ni baranka, tun ina saurayi nake tsoron Ubangiji.
13 Ashe, ba ka ji ba? Na kasa annabawan Ubangiji biyu, na ɓoye su a kogo hamsin hamsin, sa’ad da Yezebel ta kashe annabawan Ubangiji, na ciyar da su, na kuma shayar da su.
14 Yanzu kuwa ka ce, in tafi in faɗa wa sarki Ahab, cewa ga ka nan, ai, zai kashe ni.”
15 Iliya kuwa ya ce, “Na rantse da ran Ubangiji Mai Runduna, wanda nake tsaye a gabansa, hakika zan nuna kaina gare shi yau.”
16 Saboda haka sai Obadiya ya tafi wurin Ahab ya faɗa masa, Ahab kuwa ya tafi wurin Iliya.
17 Sa’ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Kai ne, wanda kake wahalar da Isra’ila?”
18 Iliya kuwa ya amsa ya ce, “Ban wahalar da Isra’ila ba, kai ne da tsohonka, gama kuna ƙin bin umarnan Ubangiji, kuna yi wa Ba’al sujada.
19 Yanzu fa ka aika a tattara mini Isra’ila duka a dutsen Karmel, da annabawan Ba’al, su ɗari huɗu da hamsin, da annabawan Ashtarot kuma, su ɗari huɗu waɗanda Yezebel take kula da su.”
Iliya da Annabawan Ba’al
20 Sai Ahab ya aika wa dukan jama’ar Isra’ila, ya tattara annabawa ɗin tare da su a dutsen Karmel.
21 Iliya kuwa ya zo kusa da jama’a ya ce, “Har yaushe za ku daina yawo da hankalinku? Idan Ubangiji shi ne Allah, to, ku bauta masa, in kuwa Ba’al ne Allah, to, ku bauta masa.” Mutane duk suka yi tsit, ba su ce uffan ba.
22 Sa’an nan ya ce wa jama’a, “Ni kaɗai ne annabin Ubangiji da ya ragu, amma annabawan Ba’al ɗari huɗu ne da hamsin.
23 To, a ba mu bijimi biyu, su su zaɓi guda su yanyanka gunduwa gunduwa, su shimfiɗa a kan itacen wuta, amma kada su kunna masa wuta. Ni kuma zan shirya ɗaya bijimin, in shimfiɗa bisa itacen wuta ba kuwa zan kunna masa wuta ba.
24 Za ku yi kira ga sunan Ba’al naku, ni kuma zan kira ga sunan Ubangiji. Allahn da ya amsa da wuta, shi ne Allah.”
Jama’a duka suka yi sowar nuna yarda da wannan.
25 Sa’an nan Iliya ya ce wa annabawan Ba’al, “Ku zaɓi bijimi guda, ku shirya shi da farko, gama kuna da yawa, sa’an nan ku yi kira ga sunan Ba’al ɗinku, amma fa kada ku kunna wuta. ”
26 Suka kuwa kama bijimin da aka ba su, suka gyara shi suka yi ta kira ga sunan Ba’al tun da safe, har tsakar ranar suna ta cewa, “Ya Ba’al, ka amsa mana!” Amma ba murya, ba kuwa wanda ya amsa. Suka yi ta tsalle a wajen bagaden da suka gina.
27 Da rana ta yi tsaka sai Iliya ya yi musu ba’a, ya ce musu, “Ku kira da babbar murya, gama shi wani allah ne, watakila yana tunani ne, ko kuwa ya zagaya ne, ko kuma ya yi tafiya. Watakila kuma yana barci ne, sai a tashe shi.”
28 Suka yi ta kira da ƙarfi bisa ga al’adarsu, suna kuma tsattsaga jikunansu da wuƙaƙe, jini yana ta zuba.
29 Suka yi ta sambatu har azahar, lokacin ba da hadaya, amma ba muryar kowa, ba amsa, ba wanda ya kula.
30 Sa’an nan Iliya ya ce wa jama’a duka su zo kusa da shi. Jama’a duka kuwa suka zo kusa da shi. Sai ya gyara bagaden Ubangiji wanda aka lalatar.
31 Ya ɗibi duwatsu goma sha biyu bisa ga yawan kabilan ‘ya’yan Yakubu, wanda Ubangiji ya ce masa, “Za a kira sunanka Isra’ila.”
32 Ya kuwa gina bagade da duwatsun da sunan Ubangiji. Ya kuma haƙa wuriya kewaye da bagaden, za ta ci kamar misalin garwar ruwa guda.
33 Ya shirya itacen wuta, ya yanyanka bijimin gunduwa gunduwa, ya shimfiɗa shi bisa itacen. Sa’an nan ya ce a cika tuluna huɗu da ruwa, a kwarara a kan hadaya ta ƙonawar da kan itacen.
34 Ya kuma sa a kwarara sau na biyu, suka kwarara sau na biyun. Ya ce kuma a kwarara sau na uku, sai suka kwarara sau na ukun.
35 Ruwa kuwa ya malale bagaden, ya cika wuriyar da aka haƙa.
36 A lokacin miƙa hadaya ta maraice, sai annabi Iliya ya matso kuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra’ila, bari ya zama sananne a wannan rana, cewa kai ne Allah a Isra’ila, ni kuma bawanka ne, na yi waɗannan abubuwa duka bisa ga maganarka.
37 Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, domin waɗannan mutane su sani, kai Ubangiji, kai ne Allah, kai ne kuma ka juyo da zuciyarsu.”
38 Ubangiji kuwa ya sa wuta ta faɗo, ta cinye hadaya ta ƙonawa, da itacen, da duwatsun, da ƙurar, ta kuma lashe ruwan da yake cikin wuriyar.
39 Sa’ad da dukan mutane suka ga haka, sai suka rusuna suka sunkuyar da kai suka ce, “Ubangiji shi ne Allah, Ubangiji shi ne Allah.”
40 Iliya kuma ya ce musu, “Ku kama annabawan Ba’al, kada ku bar ko ɗaya ya tsere.” Iliya kuwa ya kai su rafin Kishon, ya karkashe su a can.
Ƙarshen Fari
41 Iliya kuwa ya ce wa Ahab, “Sai ka haura ka ci ka sha, gama akwai motsin sakowar ruwan sama.”
42 Sai Ahab ya haura don ya ci ya sha, Iliya kuwa ya hau can ƙwanƙolin Karmel, ya zauna ƙasa, ya haɗa kai da gwiwa.
43 Sa’an nan ya ce wa baransa, “Ka tafi ka duba wajen teku.”
Baran kuwa ya tafi ya duba, ya komo ya ce, “Ban ga kome ba.”
Sai ya ce, “Ka yi tafiya kana dubawa, har sau bakwai.”
44 A zuwa na bakwai sai ya ce, “Na ga wani ɗan girgije kamar tafin hannu yana tasowa daga teku.”
Iliya kuma ya ce, “Tafi, ka faɗa wa Ahab ya shirya karusarsa ya sauka don kada ruwan sama ya hana shi sauka.”
45 Jim kaɗan sai sararin sama ya yi baƙi ƙirin da gizagizai da iska, aka yi ruwan sama mai yawan gaske. Ahab kuwa ya hau karusarsa ya tafi Yezreyel.
46 Ubangiji kuwa ya saukar wa Iliya da iko, ya sha ɗamara, ya sheka a guje, ya riga Ahab isa Yezreyel.