Gargaɗin da Dawuda Ya Yi wa Sulemanu
1 Sa’ad da lokacin rasuwar Dawuda ya gabato, sai ya yi wa ɗansa Sulemanu gargaɗi na ƙarshe, ya ce,
2 “Ina gab da rasuwa yanzu. Saboda haka, ka ƙarfafa, ka yi jaruntaka.
3 Ka yi abin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka. Ka yi biyayya da dokokinsa, da umarnansa, kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, domin ka yi nasara da dukan abin da kake yi da inda ka nufa duka,
4 domin Ubangiji ya cika maganar da ya faɗa mini cewa, ‘Idan ‘ya’yanka suna lura da hanyarsu, sun yi tafiya a gabana da gaskiya da zuciya ɗaya, da dukan ransu, ba za ka rasa mutum wanda zai hau gadon sarautar Isra’ila ba.’
5 “Ka kuma san abin da Yowab ɗan Zeruya ya yi mini, yadda ya kashe shugabannin sojoji na Isra’ila su biyu, wato Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya zubar da jinin yaƙi a lokacin salama. Ya sa jinin yaƙi a kan ɗamararsa wadda take gindinsa, da kuma kan takalmansa da yake ƙafafunsa.
6 Ka san abin da za ka yi, kada ka bar shi ya mutu ta hanyar lafiya.
7 “Amma ka nuna alheri ga ‘ya’yan Barzillai daga Gileyad, ka lura da su da kyau, gama sun nuna mini alheri sa’ad da nake gudu daga ɗan’uwanka, Absalom.
8 “Ga kuma Shimai ɗan Gera, daga garin Bahurim ta Biliyaminu. Shi ne ya yi mini mugun zagi sa’ad da na tafi Mahanayim, amma sa’ad da ya zo taryata a Urdun, sai na rantse masa da Ubangiji, na ce ba zan kashe shi ba.
9 Don haka dole ka hukunta shim, ka dai san abin da za ka yi da shi, lalle ne kuma za ka ga an kashe shi.”
Rasuwar Dawuda
10 Sa’an nan Dawuda ya rasu, aka binne shi a birnin Urushalima.
11 Ya yi shekara arba’in yana sarautar Isra’ila. Ya yi mulki shekara bakwai a Hebron, sa’an nan ya yi shekara talatin da uku yana mulki a Urushalima.
12 Sulemanu kuwa ya hau gadon sarautar ubansa, Dawuda. Mulkinsa kuma ya kahu sosai.
Mutuwar Adonija
13 Sa’an nan Adonija ɗan Haggit ya tafi wurin Bat-sheba, tsohuwar Sulemanu. Ta ce masa, “Ka zo lafiya?”
Ya ce, “Lafiya lau.”
14 Sa’an nan ya ce, “Ina da wani abin da zan faɗa miki.”
Ta ce, “To, sai ka faɗa.”
15 Ya amsa ya ce, “Kin sani dai sarauta tawa ce. Ni ne kuwa mutanen Isra’ila duka suka sa zuciya zan ci sarautar, amma al’amarin ya sāke, sai sarautar ta zama ta ƙanena , gama tasa ce bisa ga nufin Allah.
16 Yanzu dai ina da roƙo guda zuwa gare ki, kada ki hana mini.”
17 Ta ce masa, “To, sai ka faɗa.”
Sai ya ce, “In kin yarda ki yi magana da sarki Sulemanu, gama ba zai ƙi jinki ba, ki ce ya ba ni yarinyar nan, Abishag, daga Shunem, ta zama matata.”
18 Bat-sheba kuwa ta ce, “Da kyau, zan yi wa sarki magana dominka.”
19 Sa’an nan Bat-sheba ta tafi wurin sarki Sulemanu don ta yi magana da shi a kan Adonija. Sarki ya tashi domin ya tarye ta. Ya rusuna mata, sa’an nan ya zauna a kujerar sarautarsa. Ya sa aka kawo mata kujera, ta kuwa zauna a wajen damansa.
20 Sai ta ce, “Ina da wani ɗan roƙo a gare ka, kada ka hana mini shi.”
Sarki ya ce mata, “Ya tsohuwata, sai ki faɗi abin da kike so, gama ba zan hana miki ba.”
21 Ta ce, “Bari a ba Adonija, ɗan’uwanka, Abishag daga Shunem, ta zama matarsa.”
22 Sai sarki Sulemanu ya amsa wa tsohuwarsa, ya ce, “Don me kika roƙar wa Adonija Abishag? Ki roƙar masa sarautar mana, gama shi wana ne, Abiyata, firist kuma, da Yowab ɗan Zeruya suna goyon bayansa.”
23 Sai sarki Sulemanu ya rantse da Ubangiji ya ce, “Allah ya kashe ni nan take idan ban sa Adonija ya biya wannan roƙo da ransa ba.
24 Ubangiji ya kafa ni sosai a gadon sarautar tsohona, Dawuda, ya kuma cika alkawarinsa, ya ba ni mulki da zuriyata. Na rantse za a kashe Adonija yau.”
25 Sai Sarki Sulemanu ya aiki Benaiya ɗan Yehoyada, ya kashe Adonija.
An Kori Abiyata an Kashe Yowab
26 Sarki kuma ya ce wa Abiyata, firist, “Ka koma ƙasarka ta gādo a Anatot, gama ka cancanci mutuwa, amma yanzu ba zan kashe ka ba domin ka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji Allah a gaban Dawuda, tsohona, domin kuma ka sha wahala duka tare da tsohona.”
27 Saboda haka Sulemanu ya kori Abiyata daga aikin firist na Ubangiji, ta haka aka cika maganar da Ubangiji ya faɗa a kan gidan Eli a Shilo.
28 Da Yowab ya ji labari, gama har shi ya goyi bayan Adonija, ko da yake bai goyi bayan Absalom ba, sai ya gudu zuwa alfarwa ta Ubangiji, ya kama zankayen bagade.
29 Sa’ad da aka faɗa wa sarki Sulemanu, Yowab ya gudu zuwa alfarwa ta Ubangiji, ga shi, yana wajen bagade, sai Sulemanu ya aiki Benaiya, ɗan Yehoyada, ya je ya kashe shi.
30 Benaiya kuwa ya tafi alfarwa ta Ubangiji, ya ce masa, “Sarki ya ce ka fito.”
Amma Yowab ya ce, “A’a, a nan zan mutu.”
Benaiya kuma ya je ya faɗa wa sarki abin da Yowab ya ce.
31 Sarki kuwa ya ce masa, “Ka yi yadda ya ce, ka kashe shi, ka binne shi, ta haka za ka kawar mana da hakkin jinin da Yowab ya zubar ba dalili.
32 Ubangiji zai ɗora masa alhakin mugayen ayyukansa, gama ya kashe mutum biyu ba da sanin tsohona Dawuda ba, waɗanda kuma suka fi shi adalci, wato Abner ɗan Ner, shugaban sojojin Isra’ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban sojojin Yahuza.
33 Don haka alhakin jininsu zai koma a kan zuriyar Yowab har abada, amma da Dawuda da zuriyarsa, da gidansa, da gadon sarautarsa, albarkar Ubangiji za ta zauna a kansu har abada.”
34 Benaiya ɗan Yehoyada kuwa ya shiga alfarwar ya kashe shi. Aka binne shi a gidansa a karkara.
35 Sa’an nan sarki ya naɗa Benaiya ɗan Yehoyada, shugaban sojoji a maimakon Yowab, ya kuma naɗa Zadok, firist, a maimakon Abiyata.
Mutuwar Shimai
36 Sai kuma sarki ya aika a kirawo Shimai. Sa’an nan ya ce masa, “Ka gina wa kanka gida a Urushalima, ka zauna a nan, kada ka fita ko kaɗan zuwa wani wuri.
37 Gama ran da ka fita, ka haye rafin Kidron, ka tabbata fa za ka mutu, alhakin jininka kuwa zai koma kanka.”
38 Shimai kuwa ya ce wa sarki, “Abin da ka faɗa daidai ne, abin da ka ce in yi, zan yi, ranka ya daɗe.” Sai Shimai ya zauna a Urushalima kwanaki da yawa.
39 Amma bayan shekara uku, sai biyu daga cikin bayin Shimai suka gudu zuwa wurin Akish ɗan Ma’aka, Sarkin Gat. Da aka faɗa wa Shimai, cewa bayinsa suna a Gat,
40 sai ya tashi, ya yi wa jakinsa shimfiɗa, ya tafi Gat wurin Akish don neman bayinsa. Ya kuwa komo da bayinsa daga Gat.
41 Da aka faɗa wa Sulemanu, cewa Shimai ya fita Urushalima, ya tafi Gat, ya komo
42 sai ya aika a kirawo Shimai, ya ce masa, “Ashe, ban sa ka ka rantse da Ubangiji ba, na kuma dokace ka da ƙarfi, cewa ka tabbata ran da ka fita zuwa ko’ina za ka mutu? Kai kuma ka ce mini, ‘Abin da ka ce daidai ne, zan yi biyayya.’
43 To, me ya sa ka karya rantsuwar da ka yi da sunan Ubangiji, da kuma umarnin da na umarce ka?”
44 Sarki kuma ya ce masa, “Ka sani sarai irin duk muguntar da ka yi wa tsohona, Dawuda. Haka kuma Ubangiji zai sāka maka bisa ga muguntarka.
45 Amma Ubangiji zai sa mini albarka, ya kuma tabbatar da gadon sarautar Dawuda har abada.”
46 Sa’an nan sarki ya umarci Benaiya ɗan Yehoyada, ya tafi, ya kashe Shimai. Yanzu sarauta ta tabbata a hannun Sulemanu.