Sulemanu ya Auri ‘Yar Fir’auna
1 Sulemanu ya gama kai da Fir’auna, Sarkin Masar, ta wurin aure, domin ya auri ‘yar Fir’auna, ya kawo ta birnin Dawuda kafin ya gama ginin gidan kansa, da Haikalin Ubangiji, da garun Urushalima.
2 Mutane suka yi ta miƙa hadayu a al’amudai dabam dabam, domin ba a gina haikalin Ubangiji ba tukuna.
3 Sulemanu ya ƙaunaci Ubangiji, ya yi tafiya bisa ga koyarwar tsohonsa, Dawuda, amma ya miƙa sadakoki da hadayu da yawa a al’amudai dabam dabam.
Addu’ar Sulemanu don Samun Hikima
4 Sarki kuwa ya tafi Gibeyon don ya miƙa hadaya, gama a can ne akwai babban al’amudi. Ya miƙa hadayu na ƙonawa guda dubu a kan wannan bagade.
5 Ubangiji kuwa ya bayyana ga Sulemanu cikin mafarki a Gibeyon da dare, ya ce masa, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”
6 Sulemanu ya amsa ya ce, “Kai ne kake nuna ƙauna mai girma a koyaushe ga bawanka Dawuda, tsohona,domin ya yi tafiya a gabanka da aminci, da adalci, da tawali’u. Kai kuwa ka tabbatar masa da wannan ƙauna mai girma, ka kuma ba shi ɗa wanda zai hau gadon sarautarsa a wannan rana.
7 Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka naɗa ni sarki, a matsayin Dawuda, tsohona, ko da yake ni yaro ne ƙarami, ban ƙware ba.
8 Ga ni kuwa a tsakiyar jama’arka wadda ka zaɓa, jama’a mai yawa wadda ba ta ƙidayuwa saboda yawansu.
9 Domin haka ka ba ni hikima ta yi wa jama’arka shari’a, domin in rarrabe tsakanin nagarta da mugunta, gama wane ni in iya mallakar jama’arka mai yawa haka?”
10 Ubangiji kuwa ya ji daɗin abin da Sulemanu ya roƙa.
11 Ya kuma ce masa. “Da yake ka roƙi wannan, ba ka roƙar wa kanka yawan kwanaki, ko wadata ba, ko kuma ran maƙiyanka, amma ka roƙa a ba ka hikima yadda za ka mallaki jama’a,
12 to, zan yi maka yadda ka roƙa, zan ba ka zuciya ta hikima da ganewa har ba wanda ya kai kamarka, ba kuwa wanda zai kai kamarka.
13 Na kuma ba ka abin da ba ka roƙa ba, wato wadata da girma. Domin haka a zamaninka ba za a sami wani sarki kamarka ba.
14 Idan za ka yi mini biyayya ka kuma kiyaye dokokina, da umarnaina kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, to, zan ba ka tsawon rai.”
15 Da Sulemanu ya farka, ashe, mafarki ne, Sa’an nan ya zo Urushalima, ya tafi ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Ya miƙa hadayu na ƙonawa, da hadayu na salama. Ya kuma yi wa dukan barorinsa biki.
Sulemanu Ya Shara’anta Mawuyaciyar Matsala
16 Wata rana waɗansu mata masu zaman kansu, su biyu, suka zo gaban sarki.
17 Sai ɗayar ta ce, “Ran sarki ya daɗe, ni da wannan mata a gida ɗaya muke zaune, sai na haifi ɗa namiji, ita kuwa tana nan a gidan.
18 Bayan kwana uku da haihuwata, ita ma sai ta haihu. Mu kaɗai ne, ba kowa tare da mu a gidan.
19 Ana nan sai ɗan wannan mata ya mutu da dare, domin ta kwanta a kansa.
20 Da tsakar daren sai ta tashi, ta ɗauke ɗana daga wurina, sa’ad da nake barci, ta kai shi gadonta, sa’an nan ta kwantar da mataccen ɗanta a wurina.
21 Sa’ad da na tashi da safe don in ba ɗana mama, sai ga shi, matacce. Da na duba sosai, sai na ga ba nawa ba ne, wanda na haifa.”
22 Amma ɗaya matar ta ce, “A’a, mai ran shi ne nawa, mataccen kuwa shi ne naki!”
Sai ta fari ta ce, “A’a, mataccen shi ne naki, mai rai ne nawa!”
Haka suka yi ta gardama a gaban sarki.
23 Sa’an nan sarki ya ce, “To, kowaccenku ta ce mai ran shi ne nata, mataccen kuwa shi ne na waccan.”
24 Sai ya umarta a kawo takobi. Da aka kawo takobin,
25 sai ya ce, “A raba ɗan nan mai rai kashi biyu, kowacce ta ɗauki rabi.”
26 Saboda zuciyar mahaifiyar ta ainihi ta cika da juyayin ɗanta, ta ce wa sarki, “Ranka ya daɗe kada a kashe yaron! A ba ta!”
Amma ɗayar ta ce, “Kada a ba kowa daga cikinmu, a ci gaba a raba shi.”
27 Sa’an nan Sulemanu ya ce, “Kada ku kashe yaron! Ku miƙa wa ta farin, ita ce mahaifiyarsa ta ainihi.”
28 Sa’ad da dukan mutanen Isra’ila suka ji shari’ar da sarki ya yanke, sai suka girmama shi ƙwarai, gama sun gane Allah ya ba shi hikimar daidaita husuma sosai.