Yarjejeniya Tsakanin Sulemanu da Hiram
1 Hiram, Sarkin Taya, ya aiki jakadunsa zuwa wurin Sulemanu, sa’ad da ya ji ya gāji tsohonsa, gama Hiram abokin Dawuda ne ƙwarai dukan kwanakinsa.
2 Sai Sulemanu ya aika wurin Hiram, ya ce,
3 “Ka sani tsohona, Dawuda, bai iya gina Haikalin yin sujada ga Ubangiji Allahnsa ba saboda fama da yaƙe-yaƙe da maƙiyan da suke kewaye da shi, kafin Ubangiji ya mallakar masa da su.
4 Amma yanzu Ubangiji Allahna ya hutasshe ni ta kowace fuska, ba fitina ko masifa.
5 Ubangiji kuma ya yi wa tsohona Dawuda alkawari ya ce, ‘Ɗanka, wanda zai gāje ka, shi zai gina mini Haikali.’ Yanzu kuwa na yi niyyar gina wannan haikali domin sujada ga Ubangiji Allahna.
6 Saboda haka sai ka sa a saro mini itatuwan al’ul na Lebanon. Barorina za su haɗu da barorinka, ni kuwa zan biya ka aikin da barorinka za su yi bisa ga yadda ka ce, gama ka sani ba wani daga cikin mutanena da ya iya saran katako kamar mutanenka.”
7 Da Hiram ya ji maganar Sulemanu, sai ya yi murna ƙwarai, ya ce, “Yabo ga Ubangiji saboda wannan rana, gama ya ba Dawuda ɗa mai hikima da zai shugabanci wannan babbar jama’a.”
8 Sa’an nan Hiram ya aika wurin Sulemanu, ya ce, “Na ji saƙonka da ka aiko mini, a shirye nake in yi maka dukan abin da kake bukata a kan katakan itacen al’ul, da na fir.
9 Barorina za su kawo su daga Lebanon zuwa teku. Zan sa a yi gadon fito da su, su bi teku zuwa inda kake so, a can mutanena za su warware su, sa’an nan naka mutane su kwashe su. Kai kuma ka ba da abinci ga mutanena.”
10 Sai Hiram ya ba Sulemanu dukan katakan itacen al’ul da na fir da yake bukata,
11 Sulemanu kuwa yakan ba Hiram alkama mudu dubu ashirin (20,000), da tattaccen man zaitun ma’auni dubu ashirin (20,000) kowace shekara domin ya ciyar da mutanensa.
12 Ubangiji kuwa ya ba Sulemanu hikima kamar yadda ya yi masa alkawari. Akwai kuma zaman lafiya tsakanin Hiram da Sulemanu, suka kuma ƙulla yarjejeniya da juna.
13 Sarki Sulemanu kuwa ya sa a yi aikin tilas daga cikin Isra’ila duka. Waɗanda aka samu da za su yi aikin tilas ɗin mutum dubu talatin (30,000) ne.
14 Ya riƙa aikawa da su zuwa Lebanon, ya raba su mutum dubu goma goma (10,000) su yi wata ɗaya ɗaya, sa’an nan su komo gida su yi wata biyu biyu. Adoniram shi ne shugaban aikin tilas ɗin.
15 Sulemanu kuma yana da mutum dubu saba’in (70,000) a ƙasar tuddai masu haƙar duwatsu, da dubu tamanin (80,000) masu ɗauko duwatsun.
16 Banda waɗannan kuma, Sulemanu ya sa shugabanni dubu uku da ɗari uku (3,300) waɗanda suke lura da aikin, da mutanen da suke yin aikin.
17 Bisa ga umarnin sarki Sulemanu suka sassaƙa manyan duwatsu kyawawa don kafa harsashin ginin Haikali.
18 Sai maginan Sulemanu, da na Hiram, da mutanen Gebal suka shirya duwatsu da katakai da za a gina Haikalin.