Sulemanu Ya Gina Haikalin Ubangiji
1 A shekara ta arbaminya da tamanin bayan fitowar mutanen Isra’ila daga ƙasar Masar, a shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu, Sarkin Isra’ila, a watan biyu, wato watan Zib, sai Sulemanu ya fara gina Haikalin Ubangiji.
2 Haikalin da sarki Sulemanu ya gina wa Ubangiji, tsawonsa kamu sittin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kamu talatin ne.
3 Tsawon shirayin da yake a gaban Haikalin kamu ashirin ne, wato daidai da fāɗin Haikalin. Fāɗinsa kuma daga gaban Haikalin kamu goma ne.
4 Ya yi wa Haikalin tagogi, suna da fāɗi daga ciki fiye da waje.
5 Ya kuma gina bene mai ɗakuna a jikin bangon Haikalin daga gefe, da kuma bayan Haikalin, har hawa uku, kowanne kamu bakwai da rabi.
6 Fāɗin ɗakuna na ƙasa kamu biyar ne. Fāɗin ɗakunan hawa na biyu kamu shida ne. Fāɗin ɗakunan hawa na uku kuwa kamu bakwai ne. Bangaye a ƙasa sun fi na saman kauri, don ɗakunan su zauna sosai, ba tare da an kafa ginshiƙai a cikin ɗakunan ba.
7 An gina Haikalin da duwatsun da aka sassaka tun daga can wurin da aka haƙo su, don haka ba a ji amon guduma, ko na gatari, ko na wani kayan aiki irin na ƙarfe ba, sa’ad da ake ginin Haikalin.
8 Ƙofar domin ɗakuna na ƙasa tana wajen dama na Haikalin. Akwai matakai zuwa hawa na tsakiya da zuwa bene na uku.
9 Ta haka ya gina Haikalin, ya rufe shi da katakan itacen al’ul.
10 Benayen da ya gina kewaye da Haikalin, kowane bene tsayinsa kamu biyar. An haɗa su da Haikalin da katakan itacen al’ul.
11 Ubangiji ya ce wa Sulemanu,
12 “Idan ka yi biyayya da dokokina da umarnaina, to, zan cika maka alkawarin da na yi wa tsohonka Dawuda.
13 Zan zauna tare da mutanena, wato Isra’ila, a wannan Haikali da kake ginawa, ba kuwa zan taɓa rabuwa da su ba.”
14 Haka fa Sulemanu ya gama gina Haikali.
Kayan Haikali
15 Ya yi bango na ciki da katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har sama, ya kuma rufe daɓen da itacen fir.
16 Ya gina Wuri Mafi Tsarki na can ciki, ya gina shi can ƙuryar Haikalin. Tsayinsa kamu ashirin ne , an manne masa katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har sama.
17 Tsawon sauran Wuri Mafi Tsarki kuwa kamu arba’in ne.
18 Katakan itacen al’ul na cikin Haikalin, an yi musu zāne mai fasalin gora da na furanni buɗaɗɗu. An rufe bangon daga ciki duka da itacen al’ul, har ba a ganin duwatsun ginin.
19 Ya shirya Wuri Mafi Tsarki na can cikin Haikalin domin a ajiye akwatin alkawari na Ubangiji.
20 Tsawon Wuri Mafi Tsarki na can ciki kamu ashirin ne, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu ashirin. Ya dalaye shi da zinariya tsantsa. Ya kuma yi bagadensa da itacen al’ul.
21 Sulemanu ya dalaye cikin Haikalin da zinariya tsantsa. Ya kuma gifta sarƙoƙin zinariya a gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki, sa’an nan ya dalaye su da zinariya.
22 Ya dalaye dukan cikin Haikalin da zinariya, ya kuma dalaye bagaden da yake Wuri Mafi Tsarki na can ciki, da zinariya.
23 Ya yi kerubobi guda biyu da itacen zaitun, ya sa su cikin Wuri Mafi Tsarki na can ciki. Tsayin kowane kerub kamu goma ne.
24-25 Dukan kerubobin irinsu ɗaya girmansu kuma ɗaya. Tsawon kowane fiffike na kerub ɗin kamu biyar, wato tsawon daga ƙarshen wannan fiffike zuwa ƙarshen wancan fiffike kamu goma ne.
26 Tsayin kowane kerub kamu goma ne.
27 Ya sa kerubobin daura da juna a can cikin Haikali domin fikafikan su taɓi juna a tsakiya kowane ɗayan kuma ya taɓi bango.
28 Ya dalaye kerubobin da zinariya.
29 Ya zana siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a dukan bangon Haikalin, wato bango na Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki na can ciki.
30 Har daɓen ƙasa, ya dalaye shi da zinariya.
31 Ya yi ƙofa biyu na shiga Wuri Mafi Tsarki na can ciki da itacen zaitun. A saman ƙofar ya yi baka.
32 Sai ya zazzāna siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a kan ƙofofi duka biyu, sa’an nan ya dalaye duk ƙofofin da zinariya.
33 Ya yi wa Haikalin madogaran ƙofa masu ƙusurwa huɗu da itacen zaitun.
34 Ya kuma yi ƙyamare biyu a haɗe, ya yi su da itacen fir,
35 ya zazzāna ya adanta su da siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni. Sa’an nan ya dalaye su da zinariya bai ɗaya.
36 Ya gina shirayi na ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al’ul.
37 A shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu aka kafa harsashin ginin Haikalin Ubangiji a watan biyu, wato watan Zib.
38 A shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Sulemanu a watan Bul, wato watan takwas, aka gama ginin Haikalin, daidai yadda aka zayyana fasalinsa. Sulemanu ya yi shekara bakwai yana ginin Haikalin.