1 SAR 8

Sulemanu Ya Kawo Akwatin Alkawari cikin Haikali

1 Sai Sulemanu ya sa dattawan Isra’ila duka, da shugabannin kabilai, da shugabannin dangi dangi na Isra’ila, su hallara a gabansa a Urushalima, domin su kawo akwatin alkawari na Ubangiji daga Sihiyona, birnin Dawuda, zuwa Haikali.

2 Dukan jama’ar Isra’ila suka taru gaban sarki Sulemanu, wurin biki a watan Etanim, wato wata na bakwai.

3 Dukan dattawan Isra’ila suka zo, sai firistoci suka ɗauki akwatin alkawarin,

4 suka kawo tare da alfarwa ta sujada, da dukan tsarkakan tasoshin da suke cikin alfarwar. Firistoci da Lawiyawa suka kawo su.

5 Sarki Sulemanu kuwa tare da dukan taron jama’ar Isra’ila, waɗanda suka taru a gabansa, suna tare a gaban akwatin alkawari, suna ta miƙa sadakoki, da tumaki, da bijimai masu yawa, har ba su ƙidayuwa.

6 Sa’an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji suka sa a cikin Wuri Mai Tsarki na can ciki a Haikalin, a ƙarƙashin fikafikan kerubobi.

7 Gama fikafikan kerubobin suna buɗe a bisa wurin da akwatin alkawarin yake domin su rufe akwatin alkawarin da sandunansa.

8 Sandunansa suna da tsawo har ana iya ganinsu daga ɗaki na can ciki daga Wuri Mai Tsarki, amma ba a iya ganinsu daga waje. Suna nan haka har wa yau.

9 Ba kome a cikin akwatin alkawarin, sai dai alluna na dutse guda biyu waɗanda Musa ya ajiye a ciki tun a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da jama’ar Isra’ila sa’ad da suka fito daga ƙasar Masar.

10 Sa’ad da firistoci suka fito daga Wuri Mai Tsarki, sai girgije ya rufe Haikalin Ubangiji,

11 har firistoci ba su iya tsayawa su gama hidima ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika Haikalin Ubangiji.

12 Sa’an nan Sulemanu ya yi addu’a ya ce,

“Ubangiji ya ce zai zauna cikin

gizagizai masu duhu.

13 Yanzu na gina maka ɗaki mai

daraja,

Wurin da za ka zauna har abada.”

Jawabin Sulemanu ga Jama’a

14 Sa’an nan sarki Sulemanu ya juya, ya fuskanci jama’a suna tsaye, ya roƙi Allah ya sa musu albarka.

15 Ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra’ila, wanda ya cika alkawarin da ya yi wa tsohona, Dawuda, da ya ce masa,

16 ‘Tun daga ran da na fito da mutanena Isra’ila, daga Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin kabilan Isra’ila inda zan gina Haikali domin sunana ba, amma na zaɓi Dawuda ya shugabanci mutanena Isra’ilawa.’ ”

17 Sulemanu ya ci gaba, ya ce, “Tsohona, Dawuda ya yi niyyar gina wa Ubangiji Allah na Isra’ila ɗaki,

18 amma Ubangiji ya ce wa tsohona, Dawuda, ya ji daɗin niyyar da ya yi ta gina Haikali,

19 amma duk da haka ba zai gina Haikalin ba, sai ɗansa wanda za a haifa masa shi ne zai gina Haikali domin sunan Ubangiji.

20 Yanzu Ubangiji ya cika alkawarin da ya yi, gama na tashi a maimakon tsohona, Dawuda, na hau gadon sarautar Isra’ila, kamar yadda ya alkawarta, ga shi kuwa, na gina Haikali saboda Ubangiji Allah na Isra’ila.

21 A cikin Haikalin kuma na shirya wa akwatin alkawari wuri, inda alkawarin Ubangiji yake, wato alkawarin da ya yi wa kakanninmu sa’ad da ya fito da su daga ƙasar Masar.”

Addu’ar Sulemanu

22 Sa’an nan Sulemanu ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron jama’ar Isra’ila. Ya ɗaga hannuwansa sama,

23 ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra’ila, ba wani Allah kamarka cikin Sama a bisa, da cikin duniya a ƙasa, wanda yake cika alkawari, ya nuna ƙauna ga bayinsa, waɗanda suke tafiya a gabansa da zuciya ɗaya.

24 Kai wanda ka cika abin da ka faɗa wa bawanka, Dawuda, tsohona, i, abin da ka faɗa da bakinka ka cika shi yau.

25 Yanzu fa, ya Ubangiji Allah na Isra’ila, ka cika wa bawanka Dawuda, tsohona, sauran abin da ka alkawarta masa, da ka ce, ‘Ba za ka rasa mutum a gabana wanda zai hau gadon sarautar Isra’ila ba, in dai zuriyarka sun mai da hankali, sun yi tafiya a gabana kamar yadda kai ka yi.’

26 Yanzu fa, ya Allah na Isra’ila, sai ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka, Dawuda, tsohona.

27 “Amma ko Allah zai zauna a duniya? Ga shi, Saman sammai ba ta isa ta karɓe ka ba, balle wannan Haikali da na gina!

28 Duk da haka, ya Ubangiji Allahna, ka ji addu’ata, ni bawanka, da roƙe-roƙena, ka ji kukana da addu’ata da nake yi a gabanka yau.

29 Domin ka riƙa duban Haikalin nan dare da rana, wurin da ka ce sunanka zai kasance domin ka riƙa jin addu’ar da bawanka zai yi yana fuskantar wurin.

30 Sai ka riƙa jin roƙe-roƙen bawanka da na mutanenka Isra’ilawa, idan sun yi addu’a, suna fuskantar wurin nan, sa’ad da ka ji kuma, sai ka gafarta musu.

31 “Idan mutum ya yi wa maƙwabcinsa laifi, aka ba shi rantsuwa, idan ya zo, ya rantse a gaban bagadenka a wannan Haikali,

32 ya Ubangiji ka ji daga Sama, ka shara’anta bayinka, ka hukunta mai laifin, ka ɗora masa hakkinsa a kansa, amma ka kuɓutar da mara laifin, ka sāka masa bisa ga adalcinsa.

33 “Lokacin da abokan gāba suka ci mutanenka Isra’ila da yaƙi, saboda sun yi maka zunubi, idan sun komo wurinka, suka yabe ka, suka yi addu’a, suka roƙe ka a wannan Haikali,

34 sai ka ji daga Sama, ka gafarta wa jama’ar Isra’ila zunubinsu, sa’an nan ka sāke komar da su zuwa ƙasar da ka ba kakanninsu.

35 “Idan an hore su da rashin ruwan sama, saboda sun yi maka zunubi, idan sun tuba, suna fuskantar wannan Haikali, suka yi addu’a, suka kuma yabe ka,

36 sai ka ji daga Sama, ka gafarta zunuban sarki, da na jama’arka Isra’ila. Ka koya musu kyakkyawar hanyar da za su bi, ka sa a yi ruwan sama a ƙasarka wadda ka ba jama’arka gādo.

37 “Idan akwai yunwa a ƙasar, ko kuma akwai annoba, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fāri, ko tsutsa, sun cinye amfanin gona, idan kuma abokan gāba sun kawo wa jama’arka yaƙi har ƙofar birninsu, duk dai irin annoba da ciwon da yake cikinsu,

38 sai ka kasa kunne ga addu’arsu. Idan ɗaya daga cikin jama’arka Isra’ila ya matsu a zuciyarsa, ya ɗaga hannuwansa sama yana addu’a wajen wannan Haikali,

39 sai ka ji addu’arsa. Ka kasa kunne gare shi, a wurin zamanka a Sama, ka gafarta masa. Kai kaɗai ka san tunanin dukan mutane. Ka yi da kowa bisa ga abin da ya yi,

40 domin mutanenka su yi tsoronka a dukan kwanakinsu a ƙasar da ka ba kakanninmu.

41 “Sa’ad da kuma baƙo wanda yake wata ƙasa mai nisa ya ji labarin sunanka,

42 da manyan al’amura da ka yi wa jama’arka, ya zo domin ya yi maka sujada, da kuma addu’a gare ka a wannan Haikali,

43 sai ka kasa kunne ga addu’arsa. Ka ji daga Sama, wurin zamanka, ka amsa masa abin da ya roƙe ka, domin dukan mutanen duniya su san sunanka, su kuma yi tsoronka kamar jama’arka, Isra’ilawa, domin kuma su sani wannan Haikali da na gina wurin da za a yi maka sujada ne.

44 “Idan jama’arka sun tafi su yi yaƙi da abokan gābansu, idan sun yi addu’a a gare ka, suna fuskantar birnin nan da ka zaɓa, da Haikalin nan wanda na gina saboda sunanka,

45 sai ka kasa kunne ga addu’arsu. Ka ji daga sama, ka ba su nasara.

46 “Idan jama’arka sun yi maka zunubi, gama ba mutumin da ba ya yin zunubi, har ka yi fushi da su, ka kuwa bashe su a hannun abokan gāba, har suka kwashe su zuwa bauta a wata ƙasa mai nisa,

47 idan sun koma cikin hankalinsu a ƙasar da aka kai su bauta, har suka tuba, suka roƙe ka a ƙasar, suna hurta zunubansu da irin muguntar da suka aikata, ka ji addu’arsu, ya Ubangiji.

48 Idan sun komo gare ka da zuciya ɗaya, da dukan ransu a ƙasar abokan gabansu waɗanda suka kai su bauta, suka yi addu’a gare ka, suna fuskantar ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, da Haikalin da na gina saboda sunanka,

49 sai ka ji addu’arsu da roƙe-roƙensu daga Sama, wurin zamanka, ka amsa, ka ji ƙansu.

50 Ka gafarta dukan zunubansu, da tayarwar da suka yi maka. Ka sa abokan gabansu su ji tausayinsu.

51 Gama su jama’arka ne, mallakarka, waɗanda ka fito da su daga Masar, daga tsakiyar azaba.

52 “Ya Ubangiji Allah, ka dubi jama’arka Isra’ila da sarkinsu da idon rahama, ka kasa kunne gare su duk lokacin da suka yi roƙo a gare ka.

53 Gama ka keɓe su daga sauran dukan al’ummai domin su zama jama’arka kamar yadda ka faɗa ta bakin bawanka Musa, sa’ad da ka fito da kakanninmu daga Masar.”

Addu’a ta Ƙarshe

54 Da Sulemanu ya gama wannan addu’a da roƙo ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda yake a durƙushe da hannuwansa a miƙe zuwa sama.

55 Ya tsaya, ya sa wa taron jama’ar Isra’ila albarka da babbar murya, ya ce,

56 “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya hutar da jama’arsa, Isra’ilawa, bisa ga yadda ya alkawarta. Daga cikin abin da ya alkawarta duka na alheri ba ko ɗaya da bai cika ba, kamar yadda ya alkawarta wa bawansa, Musa.

57 Ya Ubangiji Allah, sai ka kasance tare da mu kamar yadda ka kasance tare da kakanninmu, kada ka rabu da mu, ko ka yashe mu.

58 Ka sa zukatanmu su juyo gare ka, mu yi tafiya cikin tafarkunka, mu kiyaye umarnanka, da ka’idodinka da dokokinka, waɗanda ka umarci kakanninmu.

59 Ya Ubangiji Allahnmu, ka sa wannan roƙo da na yi ya kasance a gabanka, dare da rana. Ka biya bukatar bawanka, da bukatar jama’arka, Isra’ila, ta kowace rana,

60 domin dukan al’umman duniya su sani Ubangiji shi kaɗai ne Allah, banda shi, ba wani.

61 Ku kuma jama’arsa, sai ku amince da Ubangiji Allahnmu da zuciya ɗaya, ku kiyaye dokokinsa da umarnansa, kamar yadda kuke yi a yau.”

An Keɓe Haikali

62 Sa’an nan sarki Sulemanu, tare da Isra’ilawa duka, suka miƙa sadaka ga Ubangiji.

63 Sulemanu kuwa ya miƙa wa Ubangiji hadaya ta salama da bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000) da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki da dukan mutanen Isra’ila suka keɓe Haikalin Ubangiji.

64 A wannan rana kuma ya keɓe tsakiyar filin da yake gaban Haikalin Ubangiji, gama a nan ne ya miƙa hadaya ta ƙonawa, da ta gari, da kitsen sadake-sadake na salama, gama bagaden tagullar da yake gaban Ubangiji ya yi ƙanƙanta ƙwarai da za a yi dukan waɗannan hadayu a kansa.

65 Sa’an nan kuma Sulemanu ya yi biki na kwana bakwai, shi da dukan jama’ar Isra’ila. Mutane suka zo, tun daga Mashigin Hamat a arewa, har zuwa iyakar ƙasar Masar a kudu, suka hallara a gaban Ubangiji Allahnmu.

66 A rana ta takwas ya sallami jama’ar, su kuwa suka yabi sarki. Sa’an nan suka kama hanyar gidajensu suna murna, suna farin ciki saboda dukan alherin da Ubangiji ya yi wa bawansa, Dawuda, da jama’arsa, Isra’ilawa.