Ubangiji Ya Sāke Bayyana ga Sulemanu
1 Da Sulemanu ya gama ginin Haikalin Ubangiji da na fāda, da dukan abin da ya so ya yi,
2 sai Ubangiji ya sāke bayyana gare shi, kamar yadda ya bayyana gare shi a Gibeyon.
3 Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu’arka da roƙe-rokenka da ka yi a gare ni, saboda haka na tsarkake Haikalin nan da ka gina, na kuma sa sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullum.
4 Amma kai, idan ka yi tafiya a gabana kamar yadda tsohonka, Dawuda, ya yi da aminci, da sahihanci, kana aikata dukan abin da na umarce ka, kana kuma kiyaye dokokina da ka’idodina,
5 sa’an nan zan kafa gadon sarautarka a bisa Isra’ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa tsohonka, Dawuda, sa’ad da na ce masa ba za a rasa mutum daga zuriyarsa wanda zai hau gadon sarautar Isra’ila ba.
6 Amma idan kai, ko ‘ya’yanka, kun bar bina, ba ku kiyaye umarnaina da dokokina ba, waɗanda na yi muku, amma kuka tafi, kuka bauta wa waɗansu gumaka, kuka yi musu sujada,
7 sai in raba jama’ar Isra’ila da ƙasar da na ba su, Haikalin kuma da na tsarkake domin sunana, zan kawar da shi daga gabana. Jama’ar Isra’ila kuwa za su zama abin karin magana, da abin ba’a a wurin dukan mutane.
8 Wannan Haikali kuwa zai zama tsibin juji, duk wanda zai wuce ta wurin, zai yi mamaki, ya yi tsaki, ya ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi wa ƙasar nan da Haikalin nan haka?’
9 Waɗansu kuwa za su amsa su ce, ‘Saboda sun bar bin Ubangiji Allahnsu wanda ya fito da kakanninsu daga ƙasar Masar, suka bi waɗansu gumaka, suka yi musu sujada, suka bauta musu, domin haka Ubangiji ya ɗora musu wannan masifa.’ ”
Sauran Ayyukan Sulemanu
10 Sulemanu ya yi shekara ashirin kafin ya gama ginin Haikalin Ubangiji da fādarsa.
11 Hiram, Sarkin Taya, kuwa ya ba Sulemanu katakan itacen al’ul da na fir da zinariya, iyakar yadda yake bukata. Sarki Sulemanu kuwa ya ba Hiram garuruwa ashirin a jihar Galili.
12 Amma sa’ad da Hiram ya zo daga Taya domin ya ga garuruwan da Sulemanu ya ba shi, sai ya ga ba su gamshe shi ba.
13 Don haka ya ce wa Sulemanu, “Dan’uwa, waɗanne irin garuruwa ke nan da ka ba ni?” Saboda haka har yanzu ana kiran ƙasar Kabul, wato marar amfani.
14 Hiram kuma ya aika wa Sulemanu da zinariya mai nauyin talanti ɗari da ashirin.
15 Wannan shi ne lissafin aikin tilas da sarki Sulemanu ya sa domin ginin Haikalin, da na fādarsa, da kuma Millo, a kuma gina garun birnin. Ya kuma sa tilas a sāke gina garuruwan Hazor, da Magiddo, da Gezer.
16 Gama Fir’auna ya haura, ya ci Gezer, ya ƙone ta da wuta, ya kuma kashe masu zama cikinta. Sa’an nan ya yi wa ‘yarsa, wato matar Sulemanu, kyauta da Gezer ɗin.
17 Sulemanu kuwa ya sāke gina Gezer. Ya kuma sa aka gina Bet-horon ta kwari ta aikin tilas,
18 da Ba’alat, da Tadmor a cikin jeji, a ƙasar Yahuza,
19 da garuruwan ajiyarsa, da garuruwan karusansa, da garuruwan mahayan dawakansa, da duk abin da Sulemanu ya so ya gina a Urushalima, da Lebanon, da dukan ƙasar da ya mallaka.
20-21 Dukan Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, da suka ragu a ƙasar, wato waɗanda ba mutanen Isra’ila ba, waɗanda mutanen Isra’ila ba su iya hallakarwa ba, Sulemanu ya sa zuriyarsu su yi aikin tilas na bauta, haka kuwa suke har wa yau.
22 Sulemanu bai mai da mutanen Isra’ila bayi ba, amma su ne sojojinsa da dogaransa, da shugabannin sojoji, da shugabannin karusansa, da mahayan dawakansa.
23 Sulemanu yana da masu lura da aiki su ɗari biyar da hamsin, suna lura da masu aikin tilas a wurare dabam dabam da ake wa Sulemanu gini.
24 Da ‘yar Fir’auna matar Sulemanu ta fita birnin Dawuda, zuwa gidan kanta wanda Sulemanu ya gina mata, sa’an nan ya gina birnin Millo.
25 Sau uku a shekara Sulemanu yakan miƙa hadayu na ƙonawa, da na salama, da hadayar turare, a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji. Ta haka aka gama ginin Haikali.
26 Sarki Sulemanu kuma ya yi jiragen ruwa a Eziyon-geber wadda take kusa da Elat, a bakin Bahar Maliya a ƙasar Edom.
27 Sarki Hiram ya aiki barorinsa, gogaggun matuƙan jiragen ruwa, da jiragen ruwa tare da barorin Sulemanu.
28 Sai suka tafi Ofir suka kawo wa sarki Sulemanu zinariya mai nauyin talanti ɗari huɗu da shirin.