Dawuda Ya Zama Sarkin Isra’ila da Yahuza
1 Dukan Isra’ilawa kuwa suka taru wurin Dawuda a Hebron, suka ce masa, “Mu ɗaya ne da kai.
2 Ko dā can lokacin da Saul yake sarauta, kai ne kake yi wa Isra’ilawa jagora zuwa yaƙi da komowa. Ubangiji Allahnka kuwa ya ce maka, ‘Za ka yi kiwon jama’ata, wato Isra’ilawa, ka kuma shugabance su.’ ”
3 Sai dattawan Isra’ilawa suka zo wurin sarki Dawuda a Hebron. Dawuda kuwa ya yi alkawari da su a Hebron a gaban Ubangiji, ake kuwa naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra’ila bisa ga faɗar Ubangiji ta bakin Sama’ila.
Dawuda Ya Ci Sihiyona
4 Sarki Dawuda kuwa, tare da dukan Isra’ilawa, suka tafi Urushalima, wato Yebus inda Yebusiyawa suke zaune.
5 Sai mazaunan Yebus, suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba.” Duk da haka Dawuda ya ci Sihiyona, gari mai kagara, wato birnin Dawuda ke nan.
6 Sai Dawuda ya ce, “Duk wanda ya ci Yebusiyawa da fari shi ne zai zama babban shugaban sojoji.” Yowab ɗan Zeruya ne ya fara tafiya, domin wannan aka maishe shi shugaba.
7 Sa’an nan Dawuda ya zauna a kagara, don haka aka kira birnin, birnin Dawuda.
8 Sai ya rutsa birnin da gini tun daga Millo. Yowab kuma ya gyaggyara sauran birnin.
9 Dawuda ya yi ta ƙasaita gaba gaba saboda Ubangiji Mai Runduna yana tare da shi.
Jarumawan Dawuda
10 Waɗannan su ne shugabanni, wato manyan jarumawan Dawuda waɗanda suka goyi bayansa sosai a mulkinsa, tare da dukan Isra’ilawa waɗanda suka naɗa shi sarki bisa ga maganar Ubangiji a kan Isra’ilawa.
11 Wannan shi ne labarin manyan jarumawan Dawuda. Yashobeyam ɗan Bahakmone shi ne shugaban jarumawa talatin. Ya karkashe mutum ɗari uku da māshinsa baki ɗaya.
12 Na biye da shi shi ne Ele’azara ɗan Dodo, Ba’ahohiye, wanda yake ɗaya daga cikin manyan jarumawan nan uku.
13 Yana tare da Dawuda a Efes-dammin sa’ad da Filistiyawa suka taru wuri ɗaya don su yi yaƙi. Akwai wata gonar sha’ir a wurin, sai jama’a suka gudu daga gaban Filistiyawa.
14 Sai shi da Dawuda suka shiga gonar sha’ir ɗin, suka tsaya ciki don su tsare ta. Suka ragargaza Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya cece su, ya ba su babbar nasara.
15 Wata rana sai uku daga cikin manyan mutanen nan talatin suka gangara zuwa dutsen Dawuda, a kogon Adullam, sa’ad da rundunar sojojin Filistiyawa suka kafa sansani a kwarin Refayawa.
16 Dawuda yana cikin kagara, sojojin Filistiyawa kuwa suna a Baitalami.
17 Sai Dawuda ya yi marmarin gida, ya ce, “Dā ma wani ya kawo mini ruwa daga rijiyar da take a ƙofar Baitalami in sha!”
18 Sai uku ɗin suka kutsa kai, suka shiga sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take a ƙofar Baitalami, suka ɗauka, suka kawo wa Dawuda, Dawuda kuwa bai sha ba, amma ya kwarara ruwan a ƙasa domin sadaka ga Ubangiji.
19 Sa’an nan ya ce, “Allah ya sawwaƙe mini da zan yi wannan abu a gabansa, da zan sha jinin waɗannan da suka sadaukar da rayukansu, gama sai da suka yi kasai da ransu, sa’an nan suka ɗebo ruwan.” Saboda haka bai sha ruwan ba. Manyan jarumawan nan uku ne suka aikata waɗannan abubuwa.
20 Abishai ɗan’uwan Yowab kuwa shi ne shugaban jarumawa talatin ɗin. Ya girgiza mashinsa, ya kashe mutum ɗari uku. Ya yi suna a cikin jarumawan nan talatin.
21 Cikin jarumawa talatin ɗin, shi ya shahara har ya zama shugabansu. Amma duk da haka bai kai ga jarumawan nan uku ba.
22 Benaiya ɗan Yehoyada, ɗan wani jarumi ne daga Kabzeyel, ya yi manyan ayyuka, ya kashe jarumawa biyu na Mowabawa. Sai ya gangara ya kashe zaki a cikin rami a ranar da ake yin dusar ƙanƙara.
23 Sai kuma ya kashe wani dogon Bamasare mai tsayi kamu biyar. Bamasaren yana da māshi mai kama da dirkar masaƙa a hannunsa, amma sai ya gangaro wurinsa da kulki a hannu, ya ƙwace māshin daga hannun Bamasaren, ya kashe shi da shi.
24 Waɗannan abubuwa Benaiya ɗan Yehoyada ya yi su, ya kuwa yi suna kamar manyan jarumawan nan uku.
25 Ya yi suna a cikin jarumawa talatin ɗin, amma bai kai ga jarumawan nan uku ba. Sai Dawuda ya sa shi ya zama shugaban matsaransa.
26-47 Waɗannan su ne manyan jarumawan sojoji.
Asahel ɗan’uwan Yowab
Elhanan ɗan Dodo daga Baitalami
Shamma daga Harod
Helez daga Felet
Aira ɗan Ikkesha daga Tekowa
Abiyezer daga Anatot
Sibbekai daga Husha
Ilai daga Aho
Maharai daga Netofa
Heled ɗan Ba’ana daga Netofa
Ittayi ɗan Ribai daga Gibeya ta Biliyaminu
Benaiya na Firaton
Hurai daga rafuffuka kusa da Ga’ash
Abiyel daga Araba
Azmawet daga Bahurim
Eliyaba daga Shalim
‘Ya’yan Yashen, maza, daga Gizon
Jonatan ɗan Shimeya daga Harod
Ahiyam ɗan Sharar daga Harod
Elifelet ɗan Ahasbai
Hefer daga Mekara
Ahaija daga Felet
Hezro daga Karmel
Nayarai ɗan Ezbai
Yowel ɗan’uwan Natan
Mibhar ɗan Hagri
Zelek daga Ammon
Naharai daga Biyerot (Mai riƙe wa Yowab ɗan Zeruya makamai)
Aira da Gareb daga Yattir
Uriya Bahitte
Zabad ɗan Alai
Adina ɗan Shiza (Shi ne shugaba a kabilar Ra’ubainu, yana da ƙungiyarsa mai soja talatin tare da shi)
Hanan ɗan Ma’aka
Yoshafat daga Mitna
Uzziya daga Ashtera
Shama da Yehiyel ‘ya’yan Hotam, maza, daga Arower
Yediyel da Yoha ‘ya’yan Shimri, maza, daga Tiz
Eliyel daga Mahawa
Yeribai, da Yoshawiya ‘ya’yan Elna’am, maza
Itma daga Mowab
Eliyel, da Obida, da Yawasiyel daga Zoba,