Mataimakan Dawuda a Ziklag
1 Mutane da yawa suka haɗa kai da Dawuda lokacin da yake a Ziklag, sa’ad da yake a takure saboda Saul ɗan Kish. Su ma suna cikin manyan jarumawan da suka taimake shi yaƙi. Dukansu gwanayen sojoji ne, suna iya su harba kibiya, ko su yi jifa da majajjawa da hannun dama ko da na hagu.
2 Su daga kabilar Biliyaminu ne, dangin Saul.
3-7 Waɗannan su ne shugabannin sojoji,
Ahiyezer, da Yowash, ‘ya’yan Shemaiya, maza, daga Gibeya
Yeziyel, da Felet, ‘ya’yan Azmawet, maza
Beraka, da Yehu daga Anatot
Ismaya daga Gibeyon babban jarumi
ne a cikin jarumawan nan talatin,
yana daga cikin shugabannin
jarumawa talatin ɗin
Irmiya, da Yahaziyel
Yohenan, da Yozabad daga Gedera
Eluzai, da Yerimot, da Be’aliya
Shemariya, da Shefatiya daga Harif
Elkana, da Isshiya, da Azarel
Yowezer, da Yashobeyam daga iyalin
Kora
Yowela, da Zabadiya ‘ya’ya maza na
Yeroham na Gedor
8 Waɗannan su ne sunayen shahararru, ƙwararrun mayaƙa daga kabilar Gad, waɗanda suka haɗa kai da sojojin Dawuda, sa’ad da yake a kagara a hamada. Su gwanayen yaƙi da garkuwa da mashi ne. Fuskokinsu kamar na zakoki, saurinsu kamar bareyi a kan dutse.
9-13 Ga yadda aka lasafta su bisa ga matsayinsu, da Ezer, da Obadiya, da Eliyab, da Mishmanna, da Irmiya, da Attai, da Eliyel, da Yohenan, da Elzabad, da Irmiya, da Makbannai.
14 Waɗannan daga kabilar Gad shugabannin sojoji ne, waɗansu na mutum dubu, sauransu kuma ƙananan shugabanni ne waɗanda suke shugabancin sojoji ɗari.
15 Su ne waɗanda suka haye Urdun a watan fari na shekara, sa’ad da Kogin Urdun ɗin ya yi ambaliya. Suka kori waɗanda suke zaune a kwaruruka, na wajen gabas da yamma da kogin.
16 Sa’an nan waɗansu daga cikin mazajen Biliyaminu da na Yahuza, suka zo wurin Dawuda a kagararsa.
17 Sai Dawuda ya fito don ya tarye su, ya ce musu, “Idan da salama kuka zo wurina don ku taimake ni, to, zuciyata za ta zama ɗaya da taku, amma idan kun zo ne don ku bashe ni ga maƙiyana, to, Allah na kakanninmu ya duba ya shara’anta, da yake ba ni da laifi.”
18 Ruhun Allah kuwa ya sauko a kan Amasa wanda daga baya ya zama shugaban talatin ɗin, sai ya ce,
“Muna tare da kai, ya Dawuda ɗan Yesse!
Allah ya ba ka nasara tare da waɗanda suke tare da kai!
Allah yana wajenka!”
Sa’an nan Dawuda ya marabce su, ya maishe su shugabanni a sojojinsa.
19 Waɗansu sojoji daga Manassa, suka tafi wurin Dawuda sa’ad da yake fita tare da Filistiyawa don su yi yaƙi da Saul. Amma Dawuda bai tafi tare da su ba, domin sarakunan Filistiyawa sun yi shawara, suka sallame shi, don kada ya juya musu gindin baka, ya nemi sulhu a wurin shugabansu Saul, da kawunansu.
20 Sa’ad da yake komawa Ziklag sai sojojin Manassa suka zo wurinsa, wato su Adana, da Yozabad, da Yediyayel, da Maikel, da Yozabad, da Elihu, da Zilletai. A sojojin kabilar Manassa, waɗannan shugabannin sojoji ne na dubu dubu.
21 Suka kuwa taimaki Dawuda sa’ad da mahara take tasar masa, gama dukansu jarumawa ne sosai, su kuma shugabannin sojoji ne.
22 Kowace rana mutane suna ta zuwa wurin Dawuda don su taimake shi, har suka zama babbar runduna.
Jerin Sojojin Dawuda a Hebron
23 Horarrun sojoji da yawa suka haɗa kai da sojojin Dawuda a Hebron domin su taimaki Dawuda da yaƙi, su mai da shi sarki maimakon Saul, kamar yadda Ubangiji ya alkawarta. Ga yadda yawansu yake.
24 Mutanen Yahuza waɗanda suke riƙe da garkuwoyi da māsu don yaƙi, mutum dubu shida da ɗari takwas (6,800).
25 Na kabilar Saminu jarumawa mayaƙa mutum dubu bakwai da ɗari (7,100).
26 Na kabilar Lawi akwai mutum dubu huɗu da ɗari shida (4,600).
27 Akwai kuma Yehoyada wanda shi ne shugaban gidan Haruna, yana da mutum dubu uku da ɗari bakwai (3,700).
28 Na dangin Zadok wanda yake jarumi, saurayi, akwai shugabannin sojoji ashirin da biyu.
29 Na kabilar Biliyaminu, wato kabilar Saul, akwai mutum dubu uku (3,000). (Har yanzu yawancin mutanen Biliyaminu ba su daina bin gidan Saul ba.)
30 Na kabilar Ifraimu akwai mutum dubu ashirin da ɗari takwas (20,800), jarumawa ne sosai, waɗanda suka shahara a danginsu.
31 Na rabin kabilar Manassa wajen yamma akwai mutum dubu goma sha takwas (18,000) waɗanda aka zaɓa domin su zo su naɗa Dawuda ya zama sarki.
32 Na kabilar Issaka akwai shugabanni ɗari biyu, waɗanda suka gane da halin da ake ciki, da abin da ya kamata Isra’ila ya yi. Su ne suke shugabancin ‘yan’uwansu.
33 Na kabilar Zabaluna akwai mutum dubu hamsin (50,000) suna da kowane irin kayan yaƙi. Suka zo domin su taimaki Dawuda da zuciya ɗaya.
34 Na kabilar Naftali akwai shugabannin sojoji dubu ɗaya (1,000) tare da sojoji dubu talatin da dubu bakwai (37,000) masu garkuwoyi da māsu.
35 Na kabilar Dan mutum dubu ashirin da takwas da ɗari shida (28,600).
36 Na kabilar Ashiru, sojoji dubu arba’in (40,000) suka fito da shirin yaƙi.
37 Kabilan gabashin Urdun, wato kabilar Ra’ubainu, da Gad, da rabin kabilar Manassa, su dubu ɗari da dubu ashirin ne (120,000), suna da kowane irin kayan yaƙi.
38 Duk waɗannan mayaƙa sun zo Hebron a shirye, da zuciya ɗaya don su naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra’ila duka. Haka kuma dukan sauran Isra’ilawa suka goyi baya da zuciya ɗaya a naɗa Dawuda ya zama sarki.
39 Suka yi kwana uku tare da Dawuda, suka yi ta ci suna sha, gama ‘yan garin sun shirya wata liyafa dominsu.
40 Waɗanda kuma suke kusa da su har zuwa Issaka, da Zabaluna da Naftali, sun kawo abinci a kan jakuna, da raƙuma, da alfadarai, da takarkarai. Suka kawo abinci mai yawa, wato gāri da kauɗar ɓaure da nonnan busassun ‘ya’yan inabi, da ruwan inabi, da man zaitun. Suka kuma kawo shanu da tumaki domin yanka a ci. Duk an yi wannan domin a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra’ila.