Dawuda Ya Yi Niyyar Kawo Akwatin Alkawari a Urushalima
1 Sa’an nan Dawuda ya yi shawara da shugabannin sojoji na dubu dubu da na ɗari ɗari, da kowane shugaba.
2 Ya kuma yi magana da dukan taron Isra’ilawa, ya ce, “Idan kun ga ya yi kyau, idan kuma nufin Ubangiji Allahnmu ne, to, bari mu aika a ko’ina wurin ‘yan’uwanmu waɗanda aka rage a ƙasar Isra’ila, mu kuma aika wa firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a biranensu masu makiyaya domin su zo wurinmu.
3 Sa’an nan mu ɗauko akwatin alkawari na Allahnmu mu kawo shi wurinmu, gama mun ƙyale shi tun zamanin Saul.”
4 Jama’a kuwa suka amince da shawarar, suka yarda kuma a yi haka ɗin.
Dawuda Ya Tafi Ya Kawo Akwatin Alkawari
5 Haka fa, Dawuda ya tattara dukan Isra’ilawa wuri ɗaya, daga Shihor ta Masar, har zuwa mashigin Hamat domin a kawo akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim.
6 Sai Dawuda tare da dukan Isra’ilawa, suka haura zuwa Ba’al, wato Kiriyat-yeyarim ta Yahuza, domin su ɗauko akwatin alkawarin Allah daga can, inda ake kira bisa sunan Ubangiji, wanda kuma yake zaune a wurin kerubobi.
7 Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah a sabon keken shanu daga gidan Abinadab. Uzza da Ahiyo suka kora keken shanun.
8 Sai Dawuda da dukan Isra’ilawa suka yi rawa da iyakar ƙarfinsu a gaban Allah, suna raira waƙoƙi suna kaɗa, garayu, da molaye, da ganguna, da kuge, suna busa ƙaho.
9 Sa’ad da suka kai masussukar Kidon, sai Uzza ya miƙa hannunsa don ya riƙe akwatin alkawarin saboda gargada.
10 Sai Ubangiji ya husata da Uzza, ya buge shi, ya mutu nan take a gaban Allah, saboda ya miƙa hannunsa ya kama akwatin alkawari.
11 Sai Dawuda ya ɓata ransa saboda da Ubangiji ya hukunta Uzza da fushi, sai ya sa wa wannan wuri suna Feresa-uzza, wato hukuncin Uzza.
12 Sa’an nan Dawuda ya ji tsoron Allah, ya ce, “Ƙaƙa zan kawo akwatin alkawarin Allah a gidana?”
13 Don haka Dawuda bai kai akwatin alkawarin zuwa cikin birninsa ba, amma ya raɓa da shi zuwa gidan Obed-edom wanda yake daga Gat.
14 Akwatin alkawarin Allah kuwa ya kasance a gidan Obed-edom har wata uku. Ubangiji kuwa ya sa wa iyalin Obed-edom da dukan abin da yake da shi albarka.