Dawuda Ya Faɗaɗa Mulkinsa
1 Bayan haka kuma Dawuda ya ci Filistiyawa da yaƙi, ya mallake su, ya ƙwace Gat da garuruwanta daga hannunsu.
2 Ya kuma ci Mowab da yaƙi, Mowabawa suka zama bayin Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji.
3 Dawuda kuma ya ci Hadadezer, Sarkin Zoba, da yaƙi a Hamat, sa’ad da ya tafi ya kafa mulkinsa a Kogin Yufiretis.
4 Sai Dawuda ya ƙwace karusai dubu (1,000), da mahayan dawakai dubu bakwai (7,000), da sojojin ƙasa dubu ashirin (20,000) daga gare shi. Dawuda kuma ya yanyanke agarar dawakan da suke jan karusai, amma ya bar waɗansu dawakai daga cikinsu waɗanda suka isa jan karusai ɗari.
5 Sa’ad da Suriyawa daga Dimashƙu suka zo don su taimaki Hadadezer Sarkin Zoba, sai Dawuda ya karkashe mutum dubu ashirin da dubu biyu (22,000) daga cikin Suriyawan.
6 Sa’an nan Dawuda ya sa ƙungiyoyin sojoji a Suriya ta Dimashƙu, Suriyawa kuma suka zama bayin Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Ubangiji kuwa ya taimaki Dawuda duk inda ya tafi.
7 Dawuda kuma ya ƙwato garkuwoyi na zinariya waɗanda barorin Hadadezer suke ɗauke da su, ya kawo su Urushalima.
8 Dawuda kuma ya kwaso tagulla mai yawan gaske daga Beta da Berotayi, biranen Hadadezer. Da su ne Sulemanu ya yi kwatarniya, da ginshiƙai, da kayayyakin Haikali.
9 Sa’ad da Toyi, Sarkin Hamat, ya ji an ce Dawuda ya riga ya ci nasara a kan sojojin Hadadezer, Sarkin Zoba,
10 sai ya aiki Adoniram ɗansa wurin sarki Dawuda, don ya gaishe shi, ya kuma yabe shi saboda ya yi yaƙi da Hadadezer, har ya ci shi, gama Hadadezer yakan yi yaƙi da Toyi. Adoniram kuwa ya kawo kayayyaki iri iri na zinariya, da na azurfa, da na tagulla.
11 Sarki Dawuda kuwa ya keɓe waɗannan ga Ubangiji, tare da azurfa da zinariya waɗanda ya kwaso daga al’umman da ya ci, wato Edom, da Mowab, da mutanen Ammon, da na Filistiya, da na Amalek.
12 Abishai ɗan Zeruya kuma ya ci nasara a kan Edomawa, mutum dubu goma sha takwas (18,000) a Kwarin Gishiri.
13 Sai ya sa ƙungiyoyin sojoji a Edom, dukan Edomawa kuma suka zama bayin Dawuda. Ubangiji kuwa ya taimaki Dawuda duk inda ya tafi.
Manyan Ma’aikatan Dawuda
14 Da haka Dawuda ya yi mulki bisa dukan Isra’ila. Ya yi wa dukan jama’arsa adalci da gaskiya.
15 Yowab ɗan Zeruya shi ne shugaban sojoji, Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci.
16 Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyata su ne firistoci, Seraiya kuwa shi ne magatakarda.
17 Benaiya ɗan Yehoyada shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato matsara. ‘Ya’yan Dawuda, maza, su ne manyan ma’aikata na kusa da shi.