Dawuda Ya Ci Rabba
1 Da bazara, lokacin da sarakuna sukan fita su yi yaƙi, sai Yowab ya tafi da sojoji suka lalatar da ƙasar Ammonawa. Suka tafi, suka kewaye Rabba da yaƙi. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima. Yowab ya bugi Rabba ya yi nasara da ita.
2 Sai Dawuda ya ciro kambi daga kan sarkinsu, sai ya iske nauyinsa talanti ɗaya na zinariya ne, akwai kuma duwatsu masu daraja a cikinsa. Dawuda ya sa kambin a kansa. Ya kwaso ganima da yawa a birnin.
3 Ya kuma fito da mutanen da suke ciki, ya yanyanka su da zartuna da makamai masu kaifi, da gatura. Haka Dawuda ya yi wa dukan biranen Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da dukan jama’a suka koma Urushalima.
Yaƙi da Gwarzayen Filistiyawa
4 Bayan wannan kuma, sai yaƙi ya tashi a Gat tsakanin Isra’ilawa da Filistiyawa, sai Sibbekai mutumin Husha ya kashe Siffai, ɗaya daga cikin zuriyar ƙattin nan. Aka ci Filistiyawa.
5 Yaƙi kuma ya sake tashi tsakanin Isra’ilawa da Filistiyawa, sai Elhanan ɗan Yayir, ya kashe Lahmi ɗan’uwan Goliyat daga Gat, wanda yake gorar mashinsa ta yi ya dirkar masaƙa.
6 Yaƙi ya sāke tashi a Gat, inda wani cindo, ƙaton mutum yake. Yana da yatsotsi ashirin da huɗu, wato a kowane hannu yana da yatsa shida, haka nan kuma a kowace ƙafarsa. Shi kuma daga zuriyar ƙattin nan ne.
7 Sa’ad da ya yi wa mutanen Isra’ila ba’a, sai Jonatan ɗan Shimeya, wato ɗan’uwan Dawuda, ya kashe shi.
8 Waɗannan uku ne Dawuda da jama’arsa suka kashe daga zuriyar ƙattin na Gat.