Dawuda Ya Danƙa Ginin Haikali ga Sulemanu
1 Dawuda ya yi umarni a tara dukan shugabannin Isra’ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin ƙungiyoyin da suke bauta wa sarki, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da masu lura da dukan dukiya da dabbobin sarki, da na ‘ya’yansa, da fādawa, da manyan sojoji, da jarumawa, a Urushalima.
2 Sarki Dawuda fa ya miƙe tsaye, ya ce, “Ku saurare ni, ku ‘yan’uwana, da jama’ata. Na yi niyya a zuciyata in gina wa akwatin alkawari na Ubangiji wurin hutawa, da wurin zaman zatin Allah. Na riga na yi shiri domin ginin,
3 amma Allah bai yardar mini in yi da kaina ba, domin ni mayaƙi ne, na kuwa zubar da jini.
4 Duk da haka Ubangiji Allah na Isra’ila ya zaɓe ni da zuriyata daga cikin gidan mahaifina, in zama Sarkin Isra’ilawa har abada. Gama shi ya zaɓi Yahuza ya zama shugaba. Daga cikin gidan Yahuza kakana, da kuma daga cikin ‘ya’yan mahaifina, maza, ya ji daɗina har ya naɗa ni sarkin dukan Isra’ila.
5 Daga cikin dukan ‘ya’yana maza, (gama Ubangiji ya ba ni ‘ya’ya maza da yawa), ya zaɓi ɗana Sulemanu ya hau gadon sarautar Isra’ila, abin mulkin Ubangiji.
6 “Ya ce mini, ‘Ɗanka Sulemanu ne zai gina Haikalina da shirayuna, gama na zaɓe shi ya zama ɗa a gare ni, ni kuwa in zama uba a gare shi.
7 Zan tabbatar da mulkinsa har abada idan ya bi umarnaina da ka’idodina da himma kamar yadda ake yi a yau.’
8 “Saboda haka a gaban dukan Isra’ila, wato taron jama’ar Ubangiji, da kuma gaban Allahnmu, sai ku kiyaye, ku bi dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki ƙasan nan mai kyau, ku kuma bar wa ‘ya’yanku ita gādo har abada.
9 “Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.
10 Ka lura, gama Ubangiji ya zaɓe ka domin ka gina Haikali, wato Wuri Mai Tsarki. Ka yi ƙarfi, ka kama aiki.”
11 Sa’an nan Dawuda ya ba ɗansa Sulemanu tsarin shirayin Haikalin, da ɗakunansa, da ɗakunan ajiya, da benaye, da Wuri Mafi Tsarki, inda ake gafarta zunubi.
12 Ya kuma ba shi tsarin dukan abin da ya yi nufin yi, na filayen Haikalin Ubangiji da dukan ɗakuna na kewaye, da ɗakunan ajiya na Haikalin Allah, da ɗakunan ajiye kyautan da aka keɓe ga Ubangiji.
13 Ya kuma ba shi tsarin ƙungiyoyin firistoci da na Lawiyawa, da na dukan hidimar da za a yi a Haikalin Ubangiji, da aikin lura da kayayyakin aiki na cikin Haikalin Ubangiji.
14 Ya kuma faɗa wa Sulemanu yawan zinariya da za a yi kwanoni da ita don yin aiki, da yawan azurfa da za a yi kwanoni da ita don yin aiki,
15 da yawan zinariya da za a yi alkukan fitilu, da kuma fitilun, da yawan zinariya da za a yi kowane alkuki da fitilunsa, da yawan azurfa da za a yi alkuki bisa ga yadda za a yi amfani da kowane alkuki,
16 da yawan zinariya da za a yi teburorin gurasar ajiyewa, da azurfar da za a yi teburorin azurfa,
17 da yawan zinariya tsantsa wadda za a yi cokula masu yatsotsi, da daruna, da finjalai, da kwanoni da ita, da yawan azurfa da za a yi kwanoni da ita,
18 da yawan zinariya tsantsa wadda za a yi bagaden ƙona turare da ita. Ya kuma ba shi tsarin zinariya ta kerubobin da za su miƙe fikafikansu su rufe akwatin alkawari na Ubangiji.
19 Sarki Dawuda ya ce, “Dukan wannan rubutacce ne daga wurin Ubangiji zuwa gare ni domin in fahimci fasalin aikin filla filla.”
20 Sarki Dawuda kuma ya ce wa ɗansa Sulemanu, “Ka yi ƙarfin hali, ka dāge sosai, ka kama aikin, kada ka ji tsoro, kada kuwa ka karai, gama Ubangiji Allah, wato Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ba, ba kuwa zai rabu da kai ba, har ka gama dukan aikin Haikalin.
21 Ga dai ƙungiyoyin firistoci da na Lawiyawa, suna nan domin yin hidima a Haikalin Allah, ga kuma gwanaye na kowace irin sana’a suna tare da kai don yin kowane irin aiki. Shugabanni da dukan jama’a suna ƙarƙashinka duka.”