Sarki Amaziya na Yahuza
1 A shekara ta biyu ta sarautar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra’ila, Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza ya ci sarauta.
2 Yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa kuwa Yehowaddin ta Urushalima.
3 Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, amma bai kai kamar kakansa Dawuda ba. Ya yi kamar yadda tsohonsa, Yowash ya yi.
4 Amma ba a kawar da wuraren yin tsafi a tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadaya, da ƙona turare a matsafai na kan tuddai.
5 Sa’ad da mulkin ya kahu sosai a hannun Amaziya, sai ya kashe fādawan da suka kashe tsohonsa.
6 Amma bai kashe ‘ya’yan masu kisankai ɗin ba, don ya bi abin da aka rubuta a littafin dokokin Musa, inda Ubangiji ya umarta cewa, “Kada a kashe iyaye saboda ‘ya’ya, kada kuma a kashe ‘ya’ya saboda iyaye, amma kowa zai mutu saboda laifin kansa.”
7 Ya kuma kashe Edomawa dubu goma (10,000) a Kwarin Gishiri, sa’an nan ya ƙwace Sela, ya ba ta suna Yokteyel, haka ake kiranta har wa yau.
8 Amaziya kuwa ya aiki manzanni wurin Yehowash, ɗan Yehowahaz, ɗan Yehu, Sarkin Isra’ila, yana nemansa da yaƙi.
9 Yehowash Sarkin Isra’ila ya mayar wa Amaziya Sarkin Yahuza da amsa cewa, “A dutsen Lebanon ƙaya ta aika wurin itacen al’ul ta ce, ‘Ka ba ɗana ‘yarka ya aura.’ Sai mugun naman jeji na Lebanon ya wuce, ya tattake ƙayar.
10 Yanzu kai, Amaziya, ka bugi Edomawa don haka zuciyarka ta kumbura. To ka gode da darajar da ka samu, ka tsaya a gida, gama don me kake tonon rikici da zai jawo maka fāduwa, kai da mutanen Yahuza?”
11 Amma Amaziya bai ji ba. Sai Yehowash Sarkin Isra’ila ya tafi, ya shiga yaƙi da Amaziya, Sarkin Yahuza a Bet-shemesh ta Yahuza.
12 Mutanen Isra’ila suka ci na Yahuza. Sai kowane mutum ya gudu gida.
13 Yehowash Sarkin Isra’ila kuwa ya kama Amaziya, Sarkin Yahuza, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya a Bet-shemesh. Ya kuma zo Urushalima ya rushe garun Urushalima kamu ɗari huɗu daga Ƙofar Ifraimu zuwa Ƙofar Kusurwa.
14 Ya kwashe dukan zinariya, da azurfa, da dukan kwanonin da suke cikin Haikalin Ubangiji, da na baitulmalin gidan sarki, da mutanen da aka ba da su jingina, sa’an nan ya koma Samariya.
15 Sauran ayyukan Yehowash da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, da yadda ya yi yaƙi da Amaziya, Sarkin Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
16 Yehowash ya mutu, aka binne shi a Samariya a makabartar sarakunan Isra’ila, Ɗansa Yerobowam na biyu ya gāji sarautarsa.
Mutuwar Sarki Amaziya na Yahuza
17 Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza, ya yi shekara goma sha biyar bayan rasuwar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra’ila.
18 Sauran ayyukan da Amaziya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
19 Aka ƙulla makirci a kansa a Urushalima, sai ya gudu zuwa Lakish, amma aka aika zuwa Lakish, aka kashe shi a can.
20 Aka kawo gawar a kan dawakai, aka binne a Urushalima a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda.
21 Sai dukan mutanen Yahuza suka ɗauki Azariya mai shekara goma sha shida, suka sarautar da shi don ya gāji tsohonsa Amaziya.
22 Shi ne ya gina Elat, ya mai da ita ta Yahuza bayan rasuwar tsohonsa.
Sarki Yerobowam na biyu na Isra’ila
23 A shekara goma sha biyar ta sarautar Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash Sarkin Isra’ila, ya ci sarauta a Samariya. Ya yi mulki shekara arba’in da ɗaya.
24 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da dukan zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra’ila su yi zunubi.
25 Ya kafa iyakar Isra’ila daga ƙofar Hamat har zuwa tekun Araba. Wannan kuwa shi ne abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa ta bakin bawansa annabi Yunana, ɗan amittai, daga Gathefer.
26 Gama Ubangiji ya ga Isra’ila tana shan azaba mai tsanani, gama ba bawa ko ɗa wanda zai taimaki Isra’ila.
27 Ubangiji kuwa bai ce zai shafe sunan Isra’ila daga duniya ba, saboda haka ya cece su ta hannun Yerobowam na biyu.
28 Sauran ayyukan Yerobowam na biyu, da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, da yaƙi da ya yi, da yadda ya ƙwato wa Isra’ila Dimashƙu da Hamat waɗanda suke na Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
29 Yerobowam na biyu kuwa ya mutu, kamar kakanninsa, sarakunan Isra’ila. Zakariya ɗansa ya gaji sarautarsa.