Sarki Manassa na Yahuza
1 Manassa yana da shekara goma sha biyu sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara hamsin da biyar yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa kuwa Hefziba.
2 Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji, gama ya aikata abubuwa masu banƙyama waɗanda al’umman da Ubangiji ya kora a gaban jama’ar Isra’ila suka aikata.
3 Gama ya gina matsafai a kan tuddai waɗanda Hezekiya tsohonsa ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba’al bagadai, ya kuma yi gunkiyan nan, wato Ashtoret, kamar yadda Ahab, Sarkin Isra’ila, ya yi. Ya yi wa taurari sujada, ya bauta musu.
4 Ya gina bagadai a Haikalin Ubangiji inda Ubangiji ya ce, “A Urushalima zan sa sunana.”
5 Ya gina wa taurarin sama bagadai a farfajiya biyu ta Haikalin Ubangiji.
6 Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa ya kuma aikata sihiri, ya yi dūba. Ya yi ma’amala da masu mabiya da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.
7 Siffar gunkiyan nan Ashtoret wadda ya yi, ya kafa ta a Haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Sulemanu, “A cikin wannan Haikali a Urushalima wadda na zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra’ila zan tabbatar da sunana har abada.
8 Ba zan sa jama’ar Isra’ila su ƙara fita daga ƙasar da na ba kakanninsu ba, idan dai za su kula su aikata dukan abin da na umarce su, su kuma kiyaye dukan dokokin da bawana Musa ya umarce su.”
9 Amma mutanen Yahuza ba su kasa kunne ba. Manassa kuma ya yaudare su, suka aikata mugunta fiye da abin da al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban jama’ar Isra’ila suka aikata.
10 Ubangiji kuwa ya yi magana ta wurin bayinsa annabawa ya ce,
11 “Tun da yake Manassa, Sarkin Yahuza, ya aikata waɗannan abubuwa masu banƙyama, ya kuma aikata mugayen abubuwa fiye da dukan abin da Amoriyawa, waɗanda suka riga shi, suka aikata, ya kuma sa mutanen Yahuza su yi zunubi saboda gumakansa,
12 saboda haka ni Ubangiji Allah na Isra’ila, zan aukar wa Urushalima da mutanen Yahuza da masifa irin wadda duk wanda ya ji labarinta, sai ya kusa suma.
13 Zan gwada Urushalima da magwajin Samariya da kuma ma’aunin gidan Ahab. Zan kuma suɗe Urushalima kamar yadda mutum yakan suɗe akushi sa’an nan ya kifar da shi.
14 Zan jefar da ragowar gādona, in bashe su a hannun abokan gāba, za su zama ganima da abin waso ga dukan abokan gābansu,
15 saboda sun aikata mugunta a gabana, suka tsokane ni in yi fushi tun ranar da kakanninsu suka fito daga Masar har wa yau.”
16 Banda wannan kuma Manassa ya kashe adalai har ya cika Urushalima daga wannan gefe zuwa wancan da jininsu, banda zunubin da ya sa mutanen Yahuza su yi, har suka aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji.
17 Sauran ayyukan Manassa, da dukan abin da ya aikata, da zunubin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
18 Manassa ya mutu, aka binne shi a lambun gidansa a gonar Uzza. Ɗansa Amon ya gāji gadon sarautarsa.
Sarki Amon na Yahuza
19 Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara biyu a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Meshullemet, ‘yar Haruz na Yotba.
20 Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa, Manassa ya yi.
21 Ya bi halin tsohonsa duka. Ya bauta wa gumakan da tsohonsa ya bauta wa, ya kuma yi musu sujada.
22 Ya rabu da Ubangiji Allah na kakanninsa, bai bi tafarkin Ubangiji ba.
23 Fādawansa kuwa suka ƙulla masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidansa.
24 Amma mutanen ƙasar suka kashe waɗannan da suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiyar. Sai suka naɗa Yosiya ɗan sarki, ya gāji tsohonsa.
25 Sauran ayyukan da Amon ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
26 Aka binne shi a kabarinsa na gonar Uzza. Ɗansa Yosiya ya gāji sarautarsa.