Sarki Yosiya na Yahuza
1 Yosiya yana da shekara takwas sa’ad da ya ci sarauta, ya yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yedida, ‘yar Adaya na Bozkat.
2 Ya yi abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji. Ya bi dukan halin kakansa, Dawuda, bai kauce dama ko hagu ba.
Yosiya da Littafin Shari’a
3 A shekara ta goma sha takwas ta sarautarsa, sai ya aiki Shafan ɗan Azaliya, wato jikan Meshullam, magatakarda, zuwa Haikalin Ubangiji, ya ce,
4 “Ka tafi wurin Hilkiya babban firist domin a lasafta yawan kuɗin da aka kawo cikin Haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tattara daga wurin jama’a.
5 A ba da kuɗin a hannun masu lura da ma’aikata waɗanda suke gyaran Haikalin Ubangiji, su kuma su ba waɗanda suke gyaran Haikalin,
6 wato masu sassaƙa, da magina, domin a sayi katako da dutsen da aka haƙo don gyaran Haikalin.
7 Kada a tambaye su yadda suka kashe kuɗin da aka sa a hannunsu, gama su amintattu ne.”
8 Hilkiya babban firist kuwa ya ce wa Shafan magatakarda, “Na iske littafin dokoki a cikin Haikalin Ubangiji.” Hilkiya kuwa ya ba Shafan littafin, shi kuwa ya karanta shi.
9 Sai Shafan magatakarda ya tafi ya faɗa wa sarki cewa, “Baranka ya kwashe kuɗin da ya tarar a Haikali, na kuwa ba masu lura da ma’aikatan Haikalin Ubangiji.”
10 Ya kuma ce wa sarki, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Ya kuwa karanta wa sarki littafin.
11 Sa’ad da sarki ya ji maganar da take cikin littafin dokoki, sai ya kece tufafinsa.
12 Sa’an nan ya umarci Hilkiya firist, da Ahikam ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mikaiya, da Shafan magatakarda, da Asaya baran sarki cewa,
13 “Ku tafi ku yi tambaya ga Ubangiji saboda ni, da jama’a, da dukan mutanen Yahuza a kan maganar littafin nan da aka samo, gama Ubangiji ya yi fushi da muƙwarai saboda kakanninmu domin ba su bi maganar littafin nan ba, har da za su yi dukan abin da aka rubuta mana.”
14 Sai Hilkiya firist, da Ahikam, da Akbor, da Shafan, da Asaya suka tafi wurin annabiya Hulda, matar Shallum ɗan Tikwa, wato jikan Harhas, mai tsaron ɗakin da ake ajiye tufafi. A Urushalima take zaune a sabuwar unguwa. Suka kuwa yi magana da ita.
15 Sai ta ce musu, “Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce, a faɗa wa mutumin da ya aiko ku gare ni,
16 ‘Ga shi, zan aukar da masifa a wurin nan, da a mazaunan wurin, bisa ga dukan maganar littafin nan wanda Sarkin Yahuza ya karanta,
17 domin sun rabu da ni, sun ƙona turare ga gumaka don su tsokane ni in yi fushi da aikin hannuwansu. Saboda haka fushina zai ƙuna a kan wurin nan, ba kuwa zai huce ba.’
18 Amma a kan Sarkin Yahuza, wanda ya aiko ku, ku tambayar masa Ubangiji, ku faɗa masa Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce, ‘A kan maganar da ka ji,
19 da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana sa’ad da ka ji yadda na yi magana gāba da wannan wuri, da kuma mazaunansa, cewa zai zama kufai da la’ana, kai kuwa ka keta tufafinka, ka yi kuka a gabana, hakika na ji kukanka.
20 Domin haka, ba za ka ga hukuncin da yake zuwa a kan Urushalima ba, za a kai ka cikin kabarinka lafiya.’ ”
Mutanen kuwa suka mayar wa sarki Yosiya da wannan magana.