Mai na Macen da Mijinta Ya Rasu
1 Matar wani daga cikin ƙungiyar annabawa da ya rasu, ta kai kuka wurin Elisha, ta ce, “Maigidana, baranka, wato mijina, ya rasu, ka kuwa sani shi mai tsoron Ubangiji ne, amma wanda yake binsa bashi ya zo zai kwashe ‘ya’yana biyu su zama bayinsa.”
2 Sai Elisha ya ce mata, “Me zan yi miki? Ki faɗa mini abin da kike da shi a gida.”
Ta ce, “Ni dai ba ni da kome a cikin gidan, sai dai kurtun mai.”
3 Sa’an nan ya ce mata, “Ki tafi ki yi aron tandaye da yawa daga maƙwabtanki waɗanda ba kome a ciki.
4 Sa’an nan ki shiga ɗaki, ke da ‘ya’yanki, ku rufe ƙofa. Ki ɗura mai cikin tandayen nan duka, bi da bi.”
5 Sai ta tashi daga wurinsa, ta tafi ta shiga ɗaki tare da ‘ya’yanta, ta rufe ƙofar. ‘Ya’yan suna kawo tandaye tana ɗurawa.
6 Da tandayen suka cika ta ce wa ɗanta, “Kawo mini wani tandu.”
Ɗan kuwa ya ce mata, “Ai, ba saura.” Sai man ya janye.
7 Sai ta koma ta faɗa wa annabi Elisha, shi kuwa ya ce mata, “Ki je ki sayar da man, ki biya bashin, abin da ya ragu kuwa ki ci, ke da ‘ya’yanki.”
Elisha da Attajira a Shunem
8 Wata rana Elisha ya wuce zuwa Shunem inda wata mace take da zama, sai ta gayyace shi cin abinci. Don haka duk lokacin da ya bi ta wannan hanya, sai ya ratsa ta gidanta, ya ci abinci.
9 Sai ta ce wa mijinta, “Na gane wannan mutum adali ne, mutumin Allah, wanda kullum yakan wuce ta hanyan nan.
10 Bari mu gina masa ɗan ɗaki a kan bene, mu sa masa gado, da tebur, da kujera, da fitila, don duk sa’ad da ya zo ya sauka a wurin.”
11 Wata rana da Elisha ya zo, ya shiga ɗakin, ya huta.
12 Sai ya ce wa baransa, Gehazi, “Kirawo matan nan.” Da ya kirawo ta, sai ta zo ta tsaya a gabansa.
13 Ya ce wa Gehazi, “Ka tambaye ta me take so in yi mata saboda dukan wannan wahala da ta yi dominmu? Tana so in yi mata magana da sarki ko da shugaban sojoji?”
Sai ta ce, “Ai, ina da dukan abin da nake bukata a cikin jama’ata.”
14 Elisha ya ce, “To, me za a yi mata?”
Sai Gehazi ya amsa ya ce, “Ai, ba ta da ɗa, mijinta kuwa tsoho ne.”
15 Sai ya ce, “Kirawo ta.” Da ya kirawo ta, sai ta zo ta tsaya a ƙofar ɗakin.
16 Elisha kuwa ya ce mata, “Baɗi war haka za ki rungumi ɗa na kanki.”
Sai ta ce, “A’a, ya shugabana, mutumin Allah, kada fa ka yi mini ƙarya.”
17 Amma macen ta sami juna biyu, ta kuwa haifi ɗa a daidai lokacin da Elisha ya faɗa mata.
18 Da yaron ya yi girma, sai wata rana ya bi mahaifinsa gona zuwa wurin masu girbi.
19 Sai ya ce wa mahaifinsa, “Wayyo, kaina, kaina.”
Uban kuwa ya ce wa baransa, “Ka ɗauke shi, ka kai shi wurin uwar.”
20 Da aka ɗauke shi, aka kai wa uwar, sai ya zauna a cinyar uwar har rana tsaka, sa’an nan ya rasu.
21 Sai ta hau, ta kwantar da shi a gadon annabi Elisha, sa’an nan ta rufe ƙofa, ta fita.
22 Sa’an nan ta aika a faɗa wa mijinta, ta ce, “Ka aiko mini ɗaya daga cikin barori da jaki domin in tafi wurin annabi Elisha, zan komo da sauri.”
23 Sai ya ce, “Me ya sa za ki tafi wurinsa yau? Ai, yau ba amaryar wata ba ce, ba kuwa ranar Asabar ba ce.”
Ita kuwa ta ce, “Ba kome, kada ka damu.”
24 Amma ta yi wa jakin shimfiɗa, ta kuma ce wa baranta, “Yi ta kora mini jakin, kada ka sassauta, sai na faɗa maka.”
25 Sai ta kama hanya, ta tafi wurin annabi Elisha a Dutsen Karmel.
Sa’ad da annabi Elisha ya gan ta zuwa, sai ya ce wa Gehazi, wato baransa, “Duba, ga Bashunemiya can.
26 Ruga ka tarye ta, ka tambayi lafiyarta, da ta mijinta, da ta ɗanta.”
Ta amsa, ta ce, “Lafiya ƙalau.”
27 Sa’ad da ta isa wurin annabi Elisha a kan dutsen, sai ta kama ƙafafunsa. Sai Gehazi ya zo zai ture ta. Amma mutumin Allah ya ce masa, “Ƙyale ta kurum, gama tana da baƙin ciki ƙwarai, Ubangiji kuwa ya ɓoye mini abin.”
28 Matar ta ce masa, “Na roƙe ka ka ba ni ɗa ne? Ashe, ban ce maka kada ka ruɗe ni ba?”
29 Elisha ya ce wa Gehazi, “Yi ɗamara, ka ɗauki sandana ka tafi. Duk wanda ka gamu da shi, kada ka gaishe shi, duk kuma wanda ya gaishe ka kada ka amsa, ka tafi ka ɗora sandana a fuskar yaron.”
30 Sai macen ta ce, “Na rantse da Ubangiji da kai kuma, ba zan bar ka ba.” Sai Elisha ya tashi, ya bi ta.
31 Gehazi kuma ya yi gaba, ya ɗora sandan a fuskar yaron, amma ba motsi ko alamar rai. Saboda haka ya koma, ya taryi Elisha, ya faɗa masa yaron bai farka ba.
32 Da Elisha ya kai ɗakin, ya ga yaron yana kwance matacce a gadonsa.
33 Sai ya shiga ya rufe ƙofa, daga shi sai yaron, ya yi addu’a ga Ubangiji.
34 Sa’an nan ya kwanta a kan yaron, ya sa bakinsa a bakin yaron, ya sa idanunsa a idanun yaron, hannuwansa kuma a kan na yaron, ya miƙe jikinsa akan yaron, sai jikin yaron ya yi ɗumi.
35 Elisha ya tashi, ya yi ta kai da komowa a cikin gidan, sa’an nan ya sāke hawan ɗakin, ya miƙe a kan yaron, sai yaron ya yi atishawa har sau bakwai, yaron kuma ya buɗe idanu.
36 Sai ya kira Gehazi ya ce, “Kirawo Bashunemiyar.” Sai ya kirawo ta. Da ta zo wurinsa, ya ce, “Ki ɗauki ɗanki.”
37 Ta kuwa zo, ta faɗi a gaban Elisha har ƙasa, sa’an nan ta ɗauki ɗanta, ta fita.
Mu’ujizai Biyu domin Annabawa
38 Elisha kuwa ya koma Gilgal sa’ad da ake fama da yunwa a ƙasar. Sa’ad da ƙungiyar annabawa suke zaune a gabansa, sai ya ce wa baransa, “Dora babbar tukunya, ka dafa wa annabawan nan fate-fate.”
39 Ɗaya daga cikinsu ya tafi saura don ya samo ganyayen ci. Sai ya ga yaɗon inabin jeji, ya ɗebo ‘ya’yan ya rungumo cike da hannu, ya zo ya yanyanka ya zuba a tukunyar abinci, ba tare da sanin ko mene ne ba.
40 Amma da suka ɗanɗana, sai suka ta da murya suka ce, “Ya mutumin Allah, akwai dafi a cikin tukunyar nan!” Ba su iya cin abincin ba.
41 Sai Elisha ya ce, “To, ku kawo gari.” Aka kawo masa, ya kuwa zuba garin a tukunyar, sa’an nan ya ce, “Ku kwaso wa mutanen. Yanzu dai kome lafiya.”
42 Wani mutum ya zo daga Ba’alshalisha ya kawo wa annabi Elisha abinci na ‘ya’yan fari, da dunƙule ashirin na sha’ir, da ɗanyun zangarkun hatsi. Sai Elisha ya ce wa baransa, ya ba ƙungiyar annabawa su ci,
43 amma baran ya ce, “Ƙaka zan raba wa mutum ɗari wannan abinci?”
Elisha ya sāke cewa, “Ka ba mutane su ci, gama Ubangiji ya ce za su ci har su bar saura.”
44 Sai ya ajiye shi a gabansu. Suka ci, suka kuwa bar saura kamar yadda Ubangiji ya faɗa.